Rikicin Mashigar Hormuz: Ƙasashen Afirka sun koma sayen fetur a matatar Dangote
[ad_1]
Wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Afirka ta Kudu, Ghana da Kenya, sun fara dogaro da matatar man Dangote da ke Najeriya domin samun man fetur, sakamakon cikas wajen jigilar mai daga Gabas ta Tsakiya.
Ƙarancin man ya samo asali ne daga rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila, Amurka, da Iran, wanda hakan ya sa aka toshe hanyar jigilar mai ta Mashigar Hormuz, wadda ta ke muhimmiyar hanyar kasuwancin mai ta duniya.
Shekaru da dama, ƙasashen Afirka sun dogara ne da matatun man Gabas ta Tsakiya.
Amma yanzu da aka samu matsala, dole ta sa suka fara neman wasu hanyoyin na daban.
A halin yanzu, matatar man Dangote, mallakar hamshaƙin attajirin nan Aliko Dangote, ita ce suka fara dogara da ita.
Matatar wadda ke Jihar Legas, tana da ƙarfin tace ɗanyen mai har ganga 650,000 a kowace rana.
Matatar mai darajar dala biliyan 20 ta fara aiki ne a shekarar 2024, kuma tana ci gaba da bunƙasa ayyukanta.
Buƙatar man fetur daga ƙasashen Afirka na ƙaruwa, inda wasu ƙasashen ma suka fara tattaunawa don ƙulla yarjejeniyar sayen man.
Wannan yanayi ya nuna yadda Afirka ta daɗe tana dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙetare, har ma da ƙasashen da suke da ɗanyen mai a ƙasa.
Misali, a baya Najeriya kan fitar da ɗanyen mai sannan ta sake sayen tataccen man da tsada daga waje.
Duk da cewa matatar Dangote na taimakawa wajen magance wannan matsala, mafi akasarin man da take tacewa a halin yanzu ana amfani da shi ne a cikin gida, yayin da kaso ƙalilan ake fitarwa zuwa sauran ƙasashen Afirka.
Masana na ganin cewa matatar ita kaɗai ba za ta iya biyan buƙatun ɗaukacin nahiyar Afirka ba, musamman ganin yadda ƙasashe da dama ba su da isassun wuraren adana man fetur.
Wasu gwamnatoci sun riga sun fara ɗaukar matakan kariya; misali, ƙasar Habasha ta buƙaci ’yan kasar da su rage amfani da motoci su koma amfani da motocin sufurin jama’a.
A Afirka ta Kudu kuwa, manyan kamfanoni na ƙoƙarin ganin sun tanadi man da zai ishi muhimman ayyukansu.
Ana sa ran buƙatar man fetur za ta ƙara tsananta, wanda hakan zai haifar da gasa tsakanin ƙasashen Afirka, sannan ya ƙara yawan ribar matatar Dangote ta ke samu.
Aliko Dangote ya bayyana cewa a halin yanzu babban ƙalubale ba batun farashi ba ne, face yadda za a samu man.
Ya kuma yi gargaɗin cewa wannan ƙaranci na mai na iya ɗaukar lokaci.
Yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙamari, ana sa ran ƙarin ƙasashen Afirka za su karkata ga matatun cikin gida irin na Dangote domin tabbatar da tsaron makamashinsu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link