Na koma jam’iyyar APC don yi wa Tinubu godiya — Fubara

[ad_1]



Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC ne, don nuna godiya ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa rawar da ya taka wajen magance rikicin siyasar jiharsa.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Hedikwatar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Gwamnan ya ce babu wanda ya tilasta masa sauya sheƙa, inda ya jaddada cewa ya koma APC a raɗin kansa.

Ya ƙara da cewa yin godiya ga shugaban ƙasa ne ya sa yanke shawarar ta zama mai sauƙi.

“Na shiga APC ne domin na gode wa Shugaban Ƙasa, sannan na haɗa kai da sauran masu ra’ayin ci gaba domin bunƙasa Jihar Ribas da Najeriya baki ɗaya. Shawara ce mai sauƙi a gare ni,” in ji shi.

Fubara, ya kuma ce bai taɓa kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar PDP ba, saboda jam’iyyar ta gaza magance matsalolin da suke damunta.

A cewarsa, mafi yawan matsalolin da ya fuskanta jam’iyyar PDP ce ta jefa shi a ciki.

“Idan zan faɗi gaskiya, ban taɓa kasancewa cikakken ɗan PDP ba. Na sha wahala sosai saboda jam’iyyar, kuma a lokacin rikicin, ban kasancewa a cikin gida ba, a waje nake.”

Sauya sheƙar gwamnan na zuwa ne bayan watanni da aka shafe ana rikicin siyasa a Jihar Ribas, wanda ya samo asali daga taƙaddama tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, kan ikon tsarin jam’iyyar a jihar.

A baya, Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan da Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida domin dawo da zaman lafiya.

Daga bisani ya mayar da Fubara kan kujerarsa, yayin da shi kuma gwamnan ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar 9 ga watan Disamba, 2025.

Gwamnan, ya ce yanzu burinsa shi ne haɗa kan mambobin APC a Jihar Ribas tare da bai wa jam’iyyar shugabanci na gari domin ci gabanta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *