Messi ya tsawaita kwantiraginsa da Inter Miami

[ad_1]

Fitaccen ɗan wasan tamaula, Lionel Messi, ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Inter Miami har zuwa shekarar 2028, kamar yadda kulob ɗin ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

Wannan sabon kwantiragin zai bai wa kulob ɗin da ma gasar MLS ta Amurka damar ci gaba da kasancewa tare da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan da duniya ta taɓa gani har zuwa ƙarshen kakar wasa ta 2028.

A ƙarshen wannan kakar ce kwataragin ɗan wasan na ƙasar Argentina zai ƙare, inda ya bayyana farin cikin sabunta shi kamar yadda wani saƙo da kulob ɗin ya wallafa a shafin X ya tabbatar.

Messi, mai shekara 38, ya koma Inter Miami ne a 2023, bayan wani lokaci mara daɗi da ya ce ya yi a ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da ke Faransa.

Da wannan sabon kwantaragin, Messi zai ci gaba da murza leda har bayan Gasar Kofin Duniya ta 2026, wadda Amurka da Kanada da kuma Mexico za su yi tarayya wajen karɓar bakuncinta.

Messi dai ya shafe mafi rinjayen shekarunsa na tamaula a Barcelona, daga shekarar 2004 har zuwa 2021, inda ya ɗauki kofin La Liga 10 da na Zakarun Turai a tsawon lokacin.

Haka kuma, a shekarar 2022 ce ya jagoranci ƙasarsa ta Argentina wadda ta lashe gasar Kofin Duniya da aka gudanar a Qatar.

A yanzu, zaƙaƙurin dan wasan ya ci ƙwallaye 114 a matakin ƙasa tare da Argentina, sannan ya dauki Copa America har sau biyu a shekarar 2021 da kuma 2024.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *