Menene Dalilin Da Ya Sa CAF Ba Ta Ɗauki Alƙalan Nijeriya A Gasar AFCON Ta 2025 Ba?
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta fitar da jerin sunayen alƙalan da za su jagoranci busa Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025, wadda za ta gudana daga 21 ga watan Disamba, 2025 zuwa 18 ga watan Janairu, 2026 a ƙasar Maroko.
An naɗa jami’ai 73, ciki har da alƙalan wasa 28, mataimakan alƙalan wasa 31, da jami’an VAR 14.
Waɗannan jami’ai suna wakiltar ƙasashe daban-daban na Afirka kuma sun yi aiki a manyan gasanni a baya.
Amma abin mamaki, babu ko ɗaya daga cikin alƙalan wasanni daga Nijeriya a cikin wannan jerin.
A maimakon haka, alƙalai daga ƙasashe kamar Chadi, Benin da Nijar sun samu wakilci.
Misali, Djindo Louis Houngnandande daga Benin da Alhadji Alaou Mahamat daga Chadi za su jagoranci wasa, yayin da wasu kamar Aymar Ayimavo Eric (mataimakin alƙalin wasa daga Benin) da Sadou Ali Brahmou (na’urar VAR daga Nijar) za su taka rawa.
Wannan lamari ya jefa tambaya a zukatan ‘yan Nijeriya.
Wasu na ganin rashin alƙalan Nijeriya ya danganci zarge-zargen karɓar cin hanci da rashawa, yayin da wasu ke ganin hakan naƙaso ne ga ƙwallon ƙafar Nijeriya.
Dukkanin alƙalan da aka zaɓa za su isa ƙasar Maroko a ranar 15 ga watan Disamba, 2025, domin samun horo kafin fara gasar.
Horon zai haɗa da duba lafiyar jiki, fasaha, da koyon ƙa’idojin wasanni don tabbatar da cewa gasar ta gudana cikin inganci.
[ad_2]
Source link