Masu yunƙurin juyin mulki sun yi niyyar kashe ni —Ministan Tsaro
[ad_1]
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (ritaya), ya bayyana cewa shi ma yana cikin jerin manyan jami’an gwamnati da aka yi niyya a kashe a yunƙurin juyin mulki da wasu hafsoshin soji suka kitsa domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
A watan Oktoba da ya gabata, rahotanni sun bayyana cewa an kama hafsoshin soji masu muƙamin Kyaftin har zuwa Birgediya-Janar, inda aka tsare su a Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji (DIA) bisa zargin shirin kifar da gwamnati.
A makon da ya gabata, Aminiya ta ruwaito cewa kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin ya mika rahotonsa ga Shugaba Tinubu.
Daga bisani, rundunar soji wadda a baya ta musanta labarin, ta tabbatar da faruwar yunƙurin juyin mulkin.
Janar Musa, wanda aka sauke daga mukamin Babban Hafsan Sojoji bayan an bankaɗo shirin, ya bayyana a shirin Sunday Politics na Channels TV cewa, “Ni ma an yi niyya a kama ni, kuma idan na ƙi, an shirya a harbe ni.”
Rahotanni sun ce akwai wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun shugabanni da aka yi niyya a kashe a wannan yunƙuri da bai yi nasara ba.
Ministan ya ƙara da cewa, da ma ’yan Najeriya ba za su amince da juyin mulkin ba, “Wannan shiri na marasa hankali ne. Idan ka duba irin mutanen da aka shirya abin da su, sai ka yi mamakin abin da ya taɓa ƙwaƙwalwarsu.
“’Yan Najeriya za su yaƙe su. Ka tuna, ’yan Najeriya sun daɗe suna gwagwarmaya da mulkin soja. Shugaban kasa ma yana cikin waɗanda suka yi wannan gwagwarmaya. Don haka tunanin cewa za su iya yin hakan a Najeriya, gaskiya suna bukatar su sake daidaita tunaninsu.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link