Mane ya kai Senegal wasan ƙarshe na AFCON

[ad_1]



Senegal ta samu nasarar kaiwa wasan ƙarshe a Gasar Kofin Afirka (AFCON) da yanzu haka take gudana a birnin Marrakesh na Morocco.

Sadio Mane ne ya jefa ƙwallon da ta bai wa Senegal nasarar doke Masar da ci 1–0 a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata a yammacin wannan Larabar.

Mane ya jefa ƙwallon ne a minti na 78 na wasan wanda Senegal ta samu mafi rinjayen kaso na mallakar ƙwallo, yayin da ita kuwa Masar ta fi mayar da hankali kan kare gida.

Sakamakon ya bai wa Senegal damar ci gaba da jan zarenta na samun galaba a kan Masar, bayan ta doke ta a wasan ƙarshe na AFCON 2022 da kuma wasannin share fagen shiga Kofin Duniya na 2022.

Tauraron Masar Mohamed Salah bai samu damar yin tasiri ba sakamakon tsauraran matakan tsaron da ’yan Senegal suka ɗauka a kansa.

A wasan, tsohon kyaftin ɗin Senegal, Kalidou Koulibaly ya samu kati na biyu a jere a gasar, lamarin da zai hana shi buga wasan ƙarshe, sannan kuma ya ji rauni har aka sauya shi.

Senegal za ta fafata a wasan ƙarshe da wadda ta yi nasara tsakanin Morocco da Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *