Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a Kano
[ad_1]
Wani magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan yadda zai jibinci lamirin hana shi ƙarin aure da matarsa ta yi a Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa magidancin dai ya ziyarci Babban Ofishin ’Yan sanda da ke Bompai domin neman shawara.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa jiya Asabar a shafinsa na Facebook.
A cewar jami’in, mutumin wanda matarsa ta hana shi ƙara aure yana neman a yi masa ƙarin haske kan abin da doka ta tanada game da amfani da kuɗi domin yi wa mai ɗakinsa dannar ƙirji.
SP Kiyawa ya ce magidancin ya je ofishin ne domin neman shawara a kan ko doka ta ba shi damar amfani da kuɗi har naira miliyan biyu wajen shawo kan matarsa dangane da buƙatarsa.
Tuni dai jama’a suka soma bayyana ra’ayoyi kan wannan mas’ala, inda wasu ke ganin hakan ya dace, wasu kuma na ba da shawarar magidancin ya bai wa dangin matar kuɗin.
Wasu ko cewa suke ai wannan wani nau’i ne na cin hanci da rashawa da dai sauransu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link