Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee

[ad_1]



Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya karɓi baƙuncin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Fadar Elysee da ke birnin Paris.

Wannan dai wani ɓangare ne na hutun aiki da Tinubun yake yi a ƙasashen Turai da ya tafi a makon jiya.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya wallafa tare da hotunan ganawar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, “Shugaba Macron ya karɓi baƙuncin Shugaba Tinubu domin cin abincin rana a fadar Elysee da ke birnin Paris.”

Tinubu ya fara hutun kwanaki 10 daga cikin hutun shekara da ya dauka wanda ya soma tun daga makon da ya gabata, inda ya bar Nijeriya a ranar Alhamis.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa zai yi hutun ne a ƙasashen Birtaniya da Faransa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *