LABARAN SAFIYAR ASSABAR 08-09-2025
Labaran Safiyar Asabar 09/08/2025CE – 15/02/1447AH Ga Takaitattun Labaran.
Jirgin Shugaban Ƙasa ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 cikin wata 18 karƙashin shugabancin Tinubu.
Wani rikici da ya ɓarke ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, tare da hallaka shanu da tumaki 39, a ƙauyen Kaduna da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi.
Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce Jonathan ne ɗan takarar da ya dace da jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Rundunar ƴan sanda ta saki ɗangwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi.
Ƴan sanda sun kama mutane 302, sun ceto mutum 50 da aka sace a jihar Katsina.
Jami’an ƴan sandan Kaduna sun cafke mutane 2 a Kurmin Kogi, bisa zargin saye da sayar da bindigogi ga ‘yan ta’adda.
Tashin Gurneti ya hallaka yara Uku a jihar Borno.
Wasu manyan kotunan jihar Gombe, karkashin jagorancin Justices H.H. Kereng da Abdulhamid Yakubu, sun yanke wa mutum 6 hukuncin daurin gidan yari bisa laifin damfara, karya amana da kuma kwaikwayon wasu mutane.
Bango ya fadowa mutum 6 kuma sun mutu, ya raunata wasu a Katsina.
Yara 3 sun gamu da ajalinsu a wani tafki a Borno.
Gwamnatin Kaduna ta amince da hutun eata 6 ga mata masu shayarwa.
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi kira da a kori Wike da Samuel Ortom da, Okezie Ikpeazu da sauran ƴan PDP da suka yi mata ungulu da kan zabo a zaɓen 2023 daga jam’iyyar.
Najeriya ta horar da Likitoci 360 don magance mutuwar mata masu juna biyu.
Ƙasar China ta mika sabon kason tallafin abinci ga Zimbabwe.
MDD ta nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ta’addanci a yankin Sahel.
Rikici ya raba aƙalla dubu 60 da muhallansu a Mozambique.
UEFA ta ci tarar Lamine Yamal da Lewandowski kan karya dokar shan kwayar kara Kuzari.
PSG na dakon tayi daga Chelsea da Manchester United ko Inter Milan kan mai tsaron ragarta, Gianluigi Donnarumma.
Ɗan wasa Jackson, baya son barin ƙungiyoyin Firimiyar Ingila ko da ya bar Chelsea a wannan kaka, kuma ana ganin Newcastle zai je.
Manchester United na nazarin sayen ɗan wasan tsakiya da kuma sabon mai tsaron raga, yayinda suke kokarin karkare tattaunawa kan, Benjamin Sesko daga RB Leipzig.
Sources
1. Leadership Hausa.
2. BBC Hausa.
3. Aminiya.
4. The Nation.
source