LABARAN YAMMACIN ALHAMIS 14-08-2025
Labaran Yammacin Alhamis 14/08/2025CE – 20/02/1447AH Ga Takaitattun Labaran.
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara.
Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne.
El-Rufai ya girgiza Kaduna yayin kamfen ɗin ɗan takarar ADC na yankin Chikun da Kajuru.
Hukumar jami’ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, sun tabbatar da mutuwar wani ɗalibi, mai suna Ajibola Ibitayo wanda ake zargin ya kashe kansa sabida faduwa jarrabawa.
Ɗan majalisar wakilai, Ibrahim Usman Auyo, mai wakiltar mazabar Hadejia, Auyo, da Kafin Hausa ta jihar Jigawa, ya yi zargin cewa, suna biyan kudi kafin a ba su damar gabatar da kudiri, ko kuma korafe-korafe a lokacin zaman majalisar.
Hukumar NDLEA a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe.
PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi.
Wani mai lalurar gani ya zama zakara a gasar wasan Chess na makarantu ta Najeriya.
An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙunan kan mutane uku.
Ƴan sanda sun kama wani fasto kan zargin ‘lakaɗa wa” yara duka a jihar Ribas.
Ambaliya ta kashe mutum aƙalla 30 a Indiya.
Harin Ukraine ya jawo gobara a matatar mai a Rasha.
Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346.
Cutar kwalara ta kashe dubban mutane a Sudan.
Akwai yiwuwar dakarun gwamnatin Syria sun aikata laifukan yaƙi.
Sudan ta Kudu ta ƙaryata tattaunawa da Isra’ila kan tsugunar da Falasɗinawa.
Ƙasashen Turai na fama da iftila’in wutar daji da tsananin zafi ya haifar.
Shugaban ƙasar Gabon ya yi wa kansa ahuwa kan juyin mulkin 2023 da ya jagoranta.
Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba.
Liverpool ta amince da siyen Giovanni Leoni daga kulob ɗin Parma, kamar yadda kociyan Liverpool ɗin Arne Slot ya bayyana.
Jamie Carragher ya ja kunnen Liverpool kan yawan kashe kuɗi da take wajen sayen ƴan wasa da cewar hakan ba shi ne tabbas ba da za ta samu damar lashe Premier League ba.
Manchester United tace ba ta matsa wa Hojlund sai ya bar ƙungiyar ba.
Sources
1. Premium Times Hausa.
2. BBC Hausa.
3. Aminiya.
4. Premium Times Hausa.
5. RFI Hausa.
source