Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya
[ad_1]
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2.
Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata.
Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na farko da ya gudanar a ranar Alhamis a kan bodar Seme.
Adenuga ya ce kayan da aka kama sun fito ne daga ƙasar Masar ta hanyar iyakar Jamhuriyar Benin, kuma an kama su ne a wani haɗin gwiwar jami’an hukumar NAFDAC.
Kwamandan ya ce an samu nasarar cafke kayan ne bisa sahihan bayanan sirri da Babban Kwamandan Kwastam, Adewale Adeniyi, da Daraktan NAFDAC, Moji Adeyeye, suka bayar.
Yayin da yake nuna kayan da aka kama, Adenuga ya ce garin fulawar an sarrafa shi ne a watan Maris 2024, kuma wa’adin amfani da shi ya kare ne a watan Nuwamba bara, yana mai cewa yana da hatsari ga lafiya ga jama’a idan aka yi amfani da shi.
“Idan aka shigo da irin waɗannan kayayyaki ƙasar nan, suna sauya buhunan su, su shigar da su kasuwa… akwai hatsari ga lafiya tattare da cin kayayyakin da suka lalace saboda za su iya haifar da cututtuka masu tsanani da sauran matsalolin lafiya na dogon lokaci.”
“Baya ga barazanar lafiya, irin waɗannan kayayyaki marasa inganci na rage darajar masana’antu na cikin gida da kuma amincewar masu saye.”
Yayin da yake bayani kan wasu kayayyakin da rundunar ta kama a watan Satumba, Adenuga ya ce rundunar ta kama fakiti 1,104 na tabar wiwi bisa bayanan sirri da ta samu.
Ya ƙara da cewa rundunar ta kama mutane biyu da fakiti 120 na maganin Tramadol.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link