Kwankwaso Ya Buƙaci Gwamnati Ta Haɗe Rundunar Tsaro Ta Jihohi Cikin Sojojin Nijeriya

[ad_1]

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta haɗe rundunar jami’an tsaro ta al’umma ta jihohi da aka ƙaddamar cikin jami’an tsaronta don ƙarfafa rundunonin sojoji da kuma magance matsalar rashin tsaro da ke ƙaruwa.

Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin bikin rantsar da mambobi 2,000 na Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Kano.

  • An Kaddamar Da Aikin Gyaran Babbar Hanyar Da Ta Hade Senegal Da Guinea-Bissau
  • ‘Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Fashi A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa na 2023 a Jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa, Nijeriya na buƙatar aƙalla ma’aikatan soja miliyan ɗaya don fuskantar ƙalubalen tsaro a faɗin ƙasar yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa, akwai nuna rashin sanin muhimmancin tsaro daga shugabannin siyasa a matakin tarayya.

“Abin da muka rasa shi ne himma daga shugabanninmu na siyasa, musamman Babban shugaban rundunar tsaron ƙasa da kansa,” in ji Kwankwaso. “Ya kamata ya tabbatar da cewa an sake horar da waɗannan sabbin jami’an, a basu kaki, da bindigu, da harsasai.”

Ya ƙara da cewa, ya kamata a haɗa ƙungiyoyin tsaro na sassan arewa da kudancin ƙasar cikin aikin soja don kawo ƙarshen abin da ya bayyana a matsayin “hauka da ke faruwa a wannan ƙasar.”

“Ina ba Gwamnatin Tarayya shawara da ta yi duk abin da za ta iya don ɗaukar waɗannan rundunonin a jihohi kamar Sokoto, Katsina, Kano da Zamfara. Wannan zai ƙara yawan jami’an tsaro a wannan ƙasar,” in ji Kwankwaso.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga sabuwar Rundunar Tsaron Al’umma da ta yi ƙoƙari na musamman don ƙarfafa wa ƙoƙarin hukumomin tsaro, musamman a yankunan kan iyaka da ke fuskantar barazanar tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *