An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob.

A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30.

A cewar mai taimaka wa ɗan majalisar, wasu mutane uku ne, da suka rufe fuskokinsu suka kai hari a ƙofar gidansa, a lokacin da suke jiran jami’an tsaronsa su buɗe kofar.

Ya bayyana cewa maharan sun ɗauke ɗan majalisar da ƙarfi daga cikin motarsa zuwa wani wuri, da ba a sani ba.

Ya ce masu garkuwar sun buqaci iyalansa su a biya su, kuɗin fansa naira miliyan hamsin.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred da Shugabannin Majalisar Jihar, har yanzu ba su ce komai ba, kan wannan al’amari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *