Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci.

A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida saboda zargin karya ƙa’idojin majalisar.

Ko da yake Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatarwar “ta yi tsauri kuma an yi ta ba bisa ƙa’ida ba.”

Da yake mayar da martani, Atiku ya ce sake buɗe ofishin ya nuna cewa ’yan Najeriya za su iya yaƙar zalunci idan suka yi tsaya tsayin daka tare.

“Abin farin ciki ne ganin an buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Duk da cewa al’ummar Kogi ta Tsakiya sun yi rashi na tsawon lokaci ba tare da wakilci ba, wannan gwagwarmaya ba ta tafi a banza ba.

“Ta tabbata cewa idan muka haɗa kai, za mu iya yaƙar zalunci,” in ji shi.

Atiku, ya danganta dakatar da Natasha a matsayin yi wa dimokuraɗiyya hawan ƙawara a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

Ya yi misali da dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, Simi Fubara, da wasu ’yan majalisa na jihar.

“Waɗannan abubuwa ba keɓantattu ba ne,” in ji shi.

“Suna nuna shirin gwamnatin Tinubu yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa; shirin raunana dimokuraɗiyya da kuma danne muryar jama’a ta kowane hali.”

Atiku ya yi alƙawarin cewa za su ci gaba da yin tsayin daka tare da yaƙar rashin adalci.

“Za mu yi amfani da duk wata hanya ta doka da dimokuraɗiyya domin kare dimokuraɗiyyarmu, kare amanar jama’a, tare da kuɓutar da ƙasarmu daga mulkin kama-karya,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *