Kashi 99.9 Na ‘Yan Bindiga A Arewa ‘Yan Nijeriya Ne
Ƙwararre a fagen sha’anin tsaro, Yahuza Getso, ya ce kusan dukkanin ‘yan bindigar da suka addabi Arewa ‘yan Nijeriya ne.
Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun riga sun san su waye da inda suke.
Getso, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
Ya ce, “Kashi 99.9 na ‘yan bindigar da ke Arewa-Masu-Gabas da Arewa ta Tsakiya ‘yan Nijeriya ne. Mun san su, mun san inda suke. Ba a ɓoye suke ba.”
Maganganunsa na zuwa be bayan sace ‘yan makaranta 25 da mahara suka yi a makarantar gwamnati a Maga, Jihar Kebbi, da kuma kisan Birigediya Janar Musa Uba a Jihar Borno.
Harin makarantar Kebbi ya faru da misalin ƙarfe 4 na Asubar ranar Litinin.
‘Yan bindigar sun shiga makarantar, sannan suka kashe mataimakiyar shugabar makarantar, sannan suka sace ‘yan mata 25.
Yanzu haka dai hukumomi na ƙara tsaurara tsaro domin ganin an ceto ɗaliban baki ɗaya da aka sace.