Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

[ad_1]


Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Jumma’a 24 ga wata cewa, Sin ta yi Allah wadai da hare-haren shafin intanet da gwamnatin Amurka take kaiwa a muhimman kayayyakin more rayuwarta, tare da daidaita hanyar sadarwar intanet a turbar da za ta aikata mummunar barna a nan gaba.

Guo Jiakun ya ce, hukumar tsaron shafin intanet ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa, abin da ake kira da “Volt Typhoon” da Amurka ta yada a baya, hakika wata manhaja ce ta tatsar kudi a fagen kasa da kasa.

A kwanan nan, wasu al’amura da suka faru masu nasaba da wannan da kasar Sin ta fitar da bayanai a kansu, sun sake tabbatar wa al’ummar duniya cewa, Amurka ita ce babbar kanwa uwar gami wajen kai hare-haren shafin intanet a duniya.

Guo ya kara da cewa, “Abubuwan da gwamnatin Amurka take aikatawa suna da yiwuwar haifar da rashin fahimta da dora laifi ga wanda bai ji ba bai gani ba, kuma kwata-kwata ba su dace ba. Kasar Sin tana kira ga Amurka ta dakatar da kai hare-haren shafin intanet kan muhimman kayayyakin more rayuwa na kasarta nan take. Bugu da kari, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don kare ‘yancin kanta na shafin intanet da kuma tsaronta yadda ya kamata.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *