KANUN LABARAN RANAR LITANIN 08-09-2025 AYI SAURARO LAFIYA



Kwamishinan ‘Yansanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ajao Adewale, ya gargadi jami’an ‘yansanda da na kula da zirga-zirga kan yin tsalle cikin motocin da ke tafe ko kuma jan sitiyarin direbobi, yana mai bayyana irin wannan hali a matsayin abin da bai da tsaro, bai dace ba, kuma yana lalata mutuncin Rundunar ‘Yansanda ta Najeriya (NPF).

Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124.

DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa yana ƙaryata Shugaba Bola Tinubu.
Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli.

Yin Ƙidaya Na Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Al’umma

Kwamishina mai wakiltar jihar Kaduna a Hukumar ƙidaya ta ƙasa, Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi ta kawo ziyara jihar Kaduna domin ganawa da shugabannin Ƙananan Hukumomin jihar 23, tare da masu ruwa da tsaki, a shirin Hukumar na wayar da kan jama’a game da ƙidayar da ke tafe.

Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno.

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU
By Uzairurb / September 7, 2025

Shugaban kungiyar Malaman jami’oi reshen jami’ar Ilorin (ASUU) Dakta Aled Akanm ya bayyana cewa wasu daga cikin Malaman jami’oin sun zama direbobin motocin Uber da kuma mabarata saboda irin yanayin rayuwar da suke fuskanta,hakan kuma ya samo asali ne kan yadda tsarin aikin nasu yake.

Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya

Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo

Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya

Ƙungiyar Izala ta tara sama da miliyan ɗari da saba’in (N170,974,512.50) sakamakon fatun layyan data gabata.

source

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *