Jami’an tsaro na iya kama ɗan uwan mai laifi idan ba a samu mai laifin ba — Lauya
[ad_1]
Wata fitacciyar lauya a Kano, Barista Asiya Muhammad Imam, wacce ke aiki a ofishin lauyoyin gwamnatin Jihar Kano da ke Gidan Murtala, ta ce doka ba ta bai wa jami’an tsaro kama ɗan uwan mai laifi idan ba a samu mai laifin ba.
Barista Asiya ta bayyana haka a yayin wani taron wayar da kan al’umma da Cibiyar Isa Wali da ke kare muradun mata, yara, matasa da nakasassu a birnin Kano da kewaye ta shirya a ranar Alhamis a unguwar Rimin Keɓe da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar.
Taron wanda ya ƙunshi nakasassu daban-daban da mata ya mayar da hankali kan tanade-tanaden Dokar ACJL ta Jihar Kano ta 2019 a ƙarƙashin shirin samar da adalci ga kowa na Justice for All (II).
A yayin taron an yi kira ga iyaye mata da su daina ɓoye laifin ’ya’yansu idan tsautsayi ya auku domin inganta tarbiyyar al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link