Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe

[ad_1]



Injin nika shinkafa ya yi ajalin wata mata mai shekaru 32, Hauwau Abubakar a kauyen Tumu da ke karamar hukumar Akkon jihar Gombe.

Lamarin ya faru a lokacin da marigayiyar mai ’ya’ya shida ta je sayen shinkafa wajen wani mai injin mai suna Muhammad Danjuma mai shekaru 29.

Bayanan Rundunar ’Yan Sandan Jihar sun nuna cewa hijabin jikinta ne ya kama bel ɗin injin, sannan ya ja ta jikinsa ya ji mata rauni a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta nan take.

Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa asibitin garin na Tumu, inda likita ya tabbatar da mutuwarta, daga nan kuma aka mika gawarta ga iyalinta domin yi mata jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Bello Yahaya, ya bayyana alhininsa tare da jajanta wa iyalan marigayiyar da al’ummar garin baki ɗaya, yana mai cewa lamarin babban rashi ne kuma mai tayar da hankali.

A wani bangare kuma, rundunar ta shawarci masu injinan nika, ma’aikata da ’yan kasuwa da su kula da ka’idojin tsaro yayin da suke aiki da irin waɗannan injinan.

Shawarwarin sun haɗa da tabbatar da kulawa yayin da injina ke aiki, da kuma hana yara kusantar irin waɗannan na’urori.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su rika bayar da rahoton rashin bin matakan tsaro wajen amfani da injina, domin kaucewa afkuwar irin wannan mummunan hatsari a nan gaba.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da cewa: “Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da tabbatar da tsaron jama’a a kowane lokaci.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *