ZAFAFAN LABARAN 10 GA WATAN SATUMBA 2025 #hausanews #bbchausa #africa



Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Mutum 9 Da Harsasai 4,264 Da Muggan Makamai A Nasarawa

Kwamishinan ‘Yansandan jihar Nasarawa CP. Shattima Muhammad ya bayyanawa manema labarai rawar da Rundunar ‘yansandan jihar suka taka wajen kama masu aikata miyagun laifuka. Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta kama mutum 9 tare da kwato harsasai 4,264 a wasu ayyukan sintiri da aka gudanar a ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara

Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara.

An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe

Rundunar ’yan sanda ta Jihar Gombe ta samu nasarori a yaƙi da masu aikata laifuka, inda ta kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Babu Shirin Gaggawa Wajen Fara Aiwatar Da Harajin Kashi 5 Na Man Fetur

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya fayyace cewa ba za a fara aiwatar da cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 nan take ba. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja.

An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi

A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya.

MDD Ta Yi Allah-wadai Da Harin Boko Haram A Bama

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta yi Allah-wadai da wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, dake yankin Bama na Jihar Borno.

Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato

Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu.

Mugunta Ba Za Ta Iya Lashe Adalci Ba

A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin duniya na kin mafarkin murdiya. Tarihi ya nuna mana cewa, tabbatar da adalci ya kasance alkiblar al’ummar dan Adam ta dindindin. Ko da yake a wani lokaci mugunta ta samu damar mai da hannun agogo baya, amma a karshe abubuwa za su koma daidai.

TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur.

Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba.

APC Ce Ke Kai Mana Hari Saboda Siyasa – Malami

Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya zargi jam’iyyar APC da amfani da ’yan daba wajen kai wa ‘ya’yan jam’iyyar ADC hari.

Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan yawan rancen da gwamnatinsa ke karɓowa.

El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙara Kan Zargin Ƴansanda Da Cin Zarafinsa A Kaduna

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Kula da Ƴansanda kan zargin wasu jami’an ƴansanda a jihar da cin zarafi da kuma amfani da muƙaminsu ba bisa ƙa’ida ba.

#hausanews #arewa #breakingnews #latestnews #nigeria #bbc #bbcnews #currentaffairs #nigerianews #hausanews #szariahausa #hausanews #bbchausa

source

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *