INEC ta yi fatali da kiraye-kirayen murabus ɗin Amupitan

[ad_1]



Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da kiran da ake yi na cewa, Shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN) ya yi murabus.

Ta bayyana irin waɗannan buƙatun a matsayin suka ga ’yancin hukumar da kundin tsarin mulki ya ba ta.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na INEC, Adedayo Oketola ya fitar a daren Alhamis a Abuja, ya ce kalaman da wasu ’yan siyasa suka yi kwanan nan na zargin shugaban da nuna ɓangaranci ba su da tushe balle makama.

Waɗannan kalaman sun biyo bayan shawarar da INEC ta yanke na bin umarnin kotun ɗaukaka ƙara da aka bayar kwanan nan.

“Hukumar INEC tana cikin waɗanda suka samar da kundin tsarin mulki. Naɗin muƙami, wa’adin aiki, da tsige Shugaba da Kwamishinonin Hukumar duk suna ƙarƙashin doka ne,” in ji sanarwar.

“Shugaban ba yana riƙe da ofis ɗin ne ba don jin daɗin kowace jam’iyyar siyasa ko wata ƙungiya. Duk wani kiran tsige shi, ba ya cikin kundin tsarin mulki, suka ce kai tsaye ga ’yancin Hukumar zaɓen ƙasar.”

INEC ta bayyana cewa, ta bi hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ne domin kauce wa sake faruwar abubuwan da suka faru a jihohin Zamfara da Filato, inda aka tsige zaɓaɓɓun jami’ai bayan da hukumar ta saɓa wa umarnin kotu.

Haka kuma, ta lura cewa yin akasin umarnin Babbar Kotun Tarayya zai iya kawo cikas ga tsarin shari’a da ake gudanarwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *