Ɗalibar BUK ta samu kyautar motar N35m a gasar MTN

[ad_1]



Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar.

Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu.

Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi.

Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce kamfanin na son tallafa wa matasa da ke karatu a manyan makarantu.

“Mun yadda da matasan Najeriya. Ba wai magana kawai muke ba, muna tare da su, muna goyon bayansu domin su zama nagartattu,” in ji shi.

Taron da aka yi a Kano ya ƙunshi rawa da waƙoƙi, wasannin kwamfuta da sauransu.

MTN ya kuma bai wa ɗalibai ’yan kasuwa 10 dandalin nuna kayayyakinsu ba tare da biyan kuɗi ba.

Ɗalibai sun bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka faranta musu rai a jami’ar, inda suka gode wa MTN saboda tallafin da suka samu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *