Hotunan ɓarnar da Iran ta yi a birnin Tel Aviv
[ad_1]
Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta mayar da martani kan sabon hari na “rigakafi” da ƙasashen Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar mata a safiyar ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra’ila da kuma wasu sasanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.
Hukumomin Iran sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare kan wasu muhimman sansanonin soja na Amurka da ke yankin Tekun Fasha.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, Iran ta kai harin ne kan waɗannan wurare:
Tashar jiragen sama ta Al-Udeid da ke Qatar
Al-Salem Air Base a Kuwait
Al-Dhafra Air Base a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
Tushen Jirgin Ruwa na Amurka na Biyar a Bahrain
Kazalika, AFP ya ruwaito cewa an ji tashin bama-bamai a babban birnin Saudiyya, Riyadh, a ranar Asabar.
Rahoton bai bayar da cikakken bayani kan inda bama-baman suka tashi ko musabbabin lamarin ba, haka kuma ba a tabbatar da asarar rayuka ko barnar dukiya ba zuwa yanzu ba.
Rahoton ya nuna cewa hare-haren na daga cikin martanin Iran kan abin da ta bayyana a matsayin barazana ga tsaronta, duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan irin barnar da aka yi ko asarar rayuka ba.
Hotunan ɓarnar da Iran hare-haren suka yi a birnin Tel Aviv na Isra’ila


Masu alaƙa
[ad_2]
Source link