’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 .

Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri.

Samamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda aka gano fakiti 3,314 na Tamuwa, wanda hakan ya sa aka kama mutum biyu.

Haka kuma, a ranar 9 ga watan Yuni, jami’an tsaro sun tsayar da wata mota a Legacy Estate, Maiduguri, inda aka gano ƙarin fakiti 4,557.

Wannan ya kai ga kama wasu mutum uku da ake zargi.

ASP Daso ya ce: “’Yan sanda ba za su lamunci karkatar da kayayyakin agaji ba, domin an tanade su ne don ceton rayuka, musamman na marasa galihu.”

An miƙa kayan da aka ƙwato ga gwamnatin Jihar Borno, ta hannun Kwamishinan Lafiya, Farfesa Baba Mallum Gana, domin raba su yadda ya dace.

A halin yanzu, an gurfanar da mutane biyar da aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *