Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano




Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya.

Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka?

Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta Mujahideen Aminudeen, ya ce masu safarar matan sun yaudarin matan da aka ceto cewa za su yi musu biza zuwa kasar Ghana inda daga nan za su wuce da su zuwa Saudiyya domin sama musu ayyukan yi.

An kana daya daga cikin mutanen ne a ranar Lahadi, wanda hakan ya kai ga cafke shugabansu da ake kira Bashir Sani Ibrahim.

Uku daga cikin matan masu shekaru 30 sn fito ne daga jihohin Kano da Jigawa a yayin da hudun mai shekara 35 da fito daga Jihar Yobe.

Dakta Aminudeen ya bayyana cewa matan sun biya mutanen Naira milian bibbyu, za su ciko Naira miliiyan 1.5 kowannensu domin sama musu biza.

Ya ce, “Wannan shi ne abin da muke ta gargadin mutane a kai — kar a yarda da tafiya ba tare da sanin inda za a kai su ba. Ana yaudarar mutane, ana kwace musu kuɗinsu, kuma da zarar sun isa ƙasashen waje ana tilasta musu shiga harkar karuwanci, fataucin miyagun ƙwayoyi ko kuma tsunduma cikin rayuwar kunci.”

Ya shawarci ’yan Najeriya da su guji irin waɗannan haɗurran tafiya, yana mai jaddada cewa kuɗin da ake ɓatawa wajen irin wannan safarar ya fi dacewa a saka shi a harkokin kasuwanci a gida.

“Da naira miliyan biyu ko uku da rabi, mutum zai iya fara kasuwanci mai kyau a Najeriya maimakon fadawa tarkon waɗannan miyagun dabaru,” in ji shi.

Ya nuna godiya cewa an samu damar dakile wannan yunkuri, yana mai cewa da masu safarar mutanen sun ci nasara, da lallai matan sun ɓace ba tare da sahu ba.

“Mun tattara bayanansu da fasfofonsu muka mika su ga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP). Za mu ci gaba da sa ido har sai an kammala bincike kan lamarin,” in ji shi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *