Gwamnatin Najeriya ta musanta biyan Boko Haram kuɗi don sakin ɗaliban Neja

[ad_1]



Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ta biya kuɗin fansa har ma ta ƙulla yarjejeniyar sakin wasu manyan kwamandojin Boko Haram gabanin ɗaliban makarantar St. Mary’s da aka sace a Jihar Neja su shaƙi iskar ’yanci.

Wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya wallafa ya yi iƙirarin cewa gwamnatin ta biya makudan kuɗaɗe domin a saki ɗalibai da malamai 230 da aka sace daga St. Mary’s Catholic School a ranar 21 ga Nuwamba.

Haka kuma, rahoton ya kuma danganta lamarin da sako wasu kwamandojin Boko Haram biyu.

Sai dai a wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya fitar ranar Talata, ya ce rahoton ya dogara ne kacokam kan majiyoyi marasa suna, lamarin da ya ce rahoton ya raina ƙwarewa da sadaukarwar jami’an tsaron ƙasar.

A cewarsa, “Domin kauce wa ruɗani, babu wani kuɗin fansa da aka biya, kuma babu wani kwamandan ‘yan ta’adda da aka sako. Zargin biyan kuɗi ta jirgin sama zuwa Gwoza labari ne ƙagagge.”

Ministan ya ƙara da cewa, rahotannin da ake yaɗawa suna cin karo da musantawar da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), har ma da Majalisar Tarayya, waɗanda duk sun fito sun ƙaryata batun biyan kuɗin fansar.

A cewarsa, ceto ɗaliban cikin aminci ba tare da asarar rai ba na da nasaba ne da ingantaccen aikin leƙen asiri da tsare-tsaren aiki da ƙwararru su gudanar.

Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin su wallafa, domin gudun ƙarfafa gwiwar masu laifi ko rage wa jami’an tsaro karsashi.

Ana iya tuna cewa, a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari makarantar kwana ta St Mary Catholic Church da ke garin Papiri na Jihar Neja.

’Yan bindigar sun sace ɗalibai da malamai fiye da 260 a lokacin harin, wanda ya ɗauki hankula a ciki da wajen Najeriya.

Sai dai cikin watan Disamba aka sako ɗaliban, a rukuni-rukuni, inda aka saki rukunin ƙarshe da ya ƙunshi ɗalibai 130, ranar 22 ga watan Disamban 2025.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin cewa ana musguna wa Kiristoci a Najeriya.

Abin da rahoton AFP ya ƙunsa

Sai dai kuma a ranar Litinin wani rahoton ya fito daga Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, wanda ya ce bincikensa ya gano cewa gwamnatin Najeriya ta biya makudan daloli a matsayin kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban makarantar St. Mary’s da aka sace a Jihar Neja.

AFP ya ambato wasu majiyoyin sirri har guda huɗu masu alaƙa da yadda aka cimma yarjejeniyar, waɗanda suka yi iƙirarin cewa gwamnatin ƙasar ta biya “maƙudan kuɗi a matsayin fansa kafin sakin ɗaliban na Papiri, bayan wata tattaunawa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranta.

Rahoton ya kuma yi zargin cewa an saki wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu a cikin ɓangaren yarjejeniyar, duk kuwa da haramcin biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga ƙarƙashin dokokin Najeriya.

A cewar AFP, an ɗauki kuɗin a jirgi mai saukar ungulu zuwa yankin Gwoza da ke Jihar Borno, a kusa da kan iyakar Kamaru, domin miƙa su ga kwamandan Boko Haram.

AFP ya ce wasu majiyoyi uku ne suka shaida masa cewa an miƙa kuɗin zuwa ga wani kwamandan Boko Haram a yankin mai suna Ali Ngulde.

Wata majiya ta ce an biya naira miliyan 40 kan kowane mutum ɗaya, kwatankwacin dala miliyan bakwai gaba ɗaya, yayin da wata ta ce adadin kuɗin gaba ɗaya ya kai naira biliyan biyu.

“Sakamakon matsalar sadarwar da aka samu a yankin, an ruwaito cewa sai da kwamandan ya tsallaka cikin Kamaru mai makwabtaka domin tabbatar da karɓar kuɗin kafin sakin rukunin farko na ɗalibai kusan 100”, a cewar AFP.

Yayin da hare-haren Boko Haram suka fi yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, tun 2009, AFP ya ruwaito cewa tsagin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin wani mutum mai suna Sadiƙu ne ya sace ɗaliban na Neja.

A baya ma an alaƙanta Sadiƙu da hannu a manyan hare-hare ciki har da harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

Kawo yanzu dai ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu — wanda rahoton ya ce shi ne ya jagoranci yarjejeniyar — bai ce komai ba game da lamarin, sai dai a baya ofishinsa ya sha musanta biyan kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *