Gwamnati Ta Musanta Biyan Kuɗin Fansa Don Sakin Ɗaliban Makaranta A Neja

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke ikirarin cewa ta biya “kudin fansa masu yawa”, ciki har da sakin kwamandojin ‘yan bindiga, don kuɓutar da ɗaliban makaranta da aka sace daga Makarantar yara ta St. Mary da ke Jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana zarge-zargen a matsayin “karya kuma ba ta da tushe” kuma cin zarafi ne ga kwarewa da mutuncin jami’an tsaron Nijeriya.

“Duk da cewa muna girmama ‘yancin ‘yan jarida, amma muna kin amincewa da wani labari da aka gina a kan majiyoyi marasa inganci da ko suna basu da shi, wadanda ba a san wake da su ba, wanda ke neman gurgunta sahihancin gwamnati mai cikakken iko da ke aiki a cikin dokokinta.

“Domin guje wa shakku, ba a biya kudin fansa ba, kuma ba a saki wani kwamandan ‘yan bindiga ba,” in ji sanarwar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *