Gwamna Bago, Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Bindiga Da Masu Ba Su Bayanai
[ad_1]
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta fuskanci ‘yan bindiga da masu ba su bayanai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wani bidiyo da Gaskiya News Hausa ta wallafa, inda ya gargadi ‘yan bindiga, masu ba su bayanai da kuma masu ba su mafaka da su bayyana kansu ga hukumomin tsaro.
- Yadda Kasar Sin Ke Tabbatar Da Babban Burinta A Aikace
- Harin Bam: Gwamnan Yobe Ya Bayar Da Tallafin ₦10m, Ya Jajantawa Al’ummar Borno
Kwanaki kadan da suka gabata, gwamnan ya ziyarci karamar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda ya tattauna da Sarkin yankin kan yadda ‘yan bindiga ke kawo cikas ga harkokin ilimi da noma.
Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma abokan hulda na kasashen waje domin karfafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda.
Ya yi takaicin yadda rashin tsaro ya yi mummunan tasiri kan ilimi da noma a jihar, yana mai cewa hare-haren ‘yan bindiga sun kawo tsaiko ga karatu da noma tare da mayar da jihar baya.
[ad_2]
Source link