Gwamna Abba K. Yusuf Ya Naɗa Mukaddashin Darakta Janar Na Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Kano
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle a matsayin Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, biyo bayan murabus ɗin Darakta Janar na hukumar, Alhaji Laminu Rabiu, wanda ya ajiye muƙaminsa a kwanaki.
Wannan naɗi na daga cikin sabbin naɗe-naɗe da ƙarin mukamai da gwamnan ya amince da su, a shirinsa na ƙarfafa manyan hukumomin gwamnati da tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da ayyuka a jihar.
- NAHCON Ta Jaddada Ƙudirinta Na Kammala Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 A Kan Lokaci
- Alhazan Nijeriya Bana Ba Za A Ba Su Guzuri A Hannu Ba, Sai Dai Su Cira Ta Katin ATM – CBN
Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
A cewar sanarwar naɗe-naɗen sun hada da:
1. Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle – Mukaddashin Darakta Janar, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano.
2. Yusuf Mukhtar – An ɗaga shi zuwa mukamin Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano.
3. Barrista Rahama Malam Alhaji – Shugabar, Cibiyar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.
4. Aina’u Ade – An ɗaga darajarta zuwa Mai taimakawa Gwamna kan Harkokin Kannywood.
Sanarwar ta bayyana cewa Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Zartarwa na Hukumar Alhazai da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar kafin ritayarsa daga aikin gwamnati. An bayyana shi a matsayin gogaggen ma’aikaci da ya shafe shekaru yana kula da harkokin aikin Hajji cikin nasara.
Game da Barrista Rahama Malam Alhaji, sanarwar ta ce ƙwararriyar lauya ce da ta shafe sama da shekaru bakwai tana aiki a fannoni daban-daban na shari’a, ciki har da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da kuma zama shugabar Tsangayar Ilimin Shari’a a Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN).
Haka kuma, ɗaga Aina’u Ade biyo bayan irin bajintar da ta nuna a tsohon muƙaminta.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci sabbin waɗanda aka naɗa da su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar aiki tukuru, gaskiya, da biyayya ga manufar “Kano Farko”. Dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.
[ad_2]
Source link