Fadar Shugaban Ƙasa Ta Zargi Turaki Da Cin Amanar Nijeriya Saboda Kiran Trump Ya Kawo Wa PDP Ɗauki
[ad_1]
Fadar Shugaban Ƙasa ta soki Shugaban PDP, Kabiru Tanimu Turaki, kan neman ɗaukin Shugaban Amurka da wasu ƙasashen Yamma da su shiga al’amuran siyasar Nijeriya.
Mai magana da yawon shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya wallafa bidiyon Turaki a shafin X, inda ya bayyana kalaman shugaban na PDP a matsayin “cin amanar kasa” saboda neman ɗaukin ƙasashen waje.
Onanuga ya rubuta, “Ba za mu taɓa mantawa da wannan bidiyo ba: ranar da wani ɗan siyasa na Nijeriya ya aikata laifin cin amanar ƙasa ta hanyar kiran ƙasashen waje su taimaka masa saboda rikicin cikin gida na jam’iyya.”
A bidiyon, Turaki ya yi magana da ’yan jarida a Abuja yayin da rikici ya ɓarke kan shugabancin PDP.
Ya ce dimokuraɗiyyar Nijeriya na cikin hatsari kuma ya roƙi Shugaba Trump da sauran ƙasashe da “ceto Nijeriya,” inda ya bayyana cewar ƙasar na fuskantar barazanar dimokuraɗiyya.
Rikicin cikin gida na ci gaba da yin ƙamari a jam’iyyar PDP, lamarin da ya sanya mutane da yawa sauya sheƙa zuwa babbar jam’iyyar adawa ta APC.
[ad_2]
Source link