Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wani mutum da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Bayo.
An cafke shi ne ranar 23 ga watan Agusta, 2025, yayin wani samame da ’yan sanda suka kai tare da haɗin gwiwar sashen leƙen asiri.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Nasiru Ibrahim da fakiti 25 na tabar wiwi.
Ragowar ƙwayoyin da aka samu a wajensa sun haɗa da fakiti 34 na ƙwayar Exzol, da kuma ƙwayar D5 guda 600.
An miƙa shi tare da kayan da aka ƙwato zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ta jaddada aniyarta na yaƙi da miyagun laifuka, musamman ta’ammali da ƙwayoyi, waɗanda ke jawo matsalolin tsaro a cikin al’umma.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link