Dambarwar Gyara Dokar Zaɓe: ‘Yan Siyasa Da Lauyoyi Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Nemi A Yi Taka-tsantsan

[ad_1]

A ranar Talatar da ta gabata ne, majalisar dattawa ta amince da tilasta aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura daga rumfunan zabe zuwa hukumar INEC ta kasa. Yayin da kuma ta ba da damar tattara sakamakon zaben a hannu a lokutan da na’urar ta gaza.

Matsayar da suka cimma, ta sauya kuri’ar da aka yi a baya, wacce ta cire tanade-tanaden watsa sakamakon zaben ta hanyar na’ura daga gyaran dokar zaben aka yi.

  • CGTN: Mafarkin Amurka Ya Lalace Zuwa Rudi Na Cin Zali
  • Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Ribas

Majalisar dattawan, ta sake gyara dokar zaben ne, domin bayar da izinin watsa sakamakon ta hanyar amfani da na’ura da kuma bayar da kariya, don magance matsalar hanyar sadarwa ko gazawar na’urar.

A karkashin sabon tanadin, an bayar da izinin watsa sakamakon ta hanyar sadarwar na’ura, amma kuma ba dole ba ne, musamman idan aka samu gazawar intanet, za a iya amfani da fom din EC8A a cika da hannu, a tattara bayanan sakamakon.

Matakin dai, ya biyo bayan kudirin da Bulaliyar Majalisa (Chief Whip), Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) ya gabatar a wani zaman taron gaggawa. Monguno ya ce, an yi gyaran ne domin a daidaita dokar zabe tare da bukatun ‘yan Nijeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya gabatar da kudirin a gaban majalisar, sannan kuma ya samu gagarumin goyon baya.

A yayin bitar na gyaran dokar zaben a makon da ya gabata, Monguno ya bukaci a ci gaba da rike sashe na 60 na dokar 2022, wanda ke ba da damar aika sakamako zuwa cibiyoyin tattara bayanai.

Har ila yau kuma, an samu rashin jituwa a lokacin da ya koma, don soke amincewar Majalisar Dattawan na Sashe na 60 (3) na Dokar Zabe (Sakewa da Amincewa), 2026, game da hanyoyin watsawa ta hanyar na’ura.

Bayan kammala zaman, Akpabio ya sanar da wani kwamiti mai dauke da wakilai 12, domin sasanta sabanin da ke tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai, a kan gyaran.

Mambobin, sun hada da Sanata Simon Bako Lalong (a matsayin shugaba), Sanata Monguno, Adamu Aliero, Orji Uzor Kalu, Abba Moro, Asukuo Ekpenyong, Aminu Iya Abbas, Tokunbo Abiru, Niyi Adegbonmire (SAN), Jibrin Isah, Ipalibo Banigo da kuma Onyekachi Nwebonyi.

Haka zalika, Akpabio ya bukaci kwamitin da ya gaggauta gudanar da aikin cikin gaggawa, inda ya bayyana fatansa na cewa; za a iya kammala aikin cikin mako guda, domin shugaba Bola Tinubu ya sa hannu a kan kudirin dokar zaben da aka yi wa kwaskwarima a wannan watan.

An gudanar da zaman taron gaggawa ne, a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da nuna rashin jin dadi kan gyare-gyaren da majalisar dattawan ta yi a baya, musamman na kawar da bukatun watsa sakamakon zabe ta na’urar zamani.

Lauyoyi Sun Bayyana Ra’ayoyin Mabambanta

‘Yan sa’o’i kadan, bayan Majalisar Dattawa ta amince da watsa sakamakon ta hanyar na’ura da kuma tattarawa da hannu a cikin dokar zabe ta 2026, wasu lauyoyi sun bayyana mabambantan ra’ayoyi kan matakin.

Yayin da wasu suka yaba da matakin, wasu kuma sun ce; akwai damar yin amfani da sakamakon ta hanyar tattarawa da hannu.

A cewarsu, a wannan zamani da duniya ta koma dijital, bai kamata Nijeriya ta rika magana a kan tattara sakamakon zabe da hannu ba.

Abdul Balogun, SAN, ya ce; kowa zai iya tunanin cewa; kasar za ta iya tafiya kafada da kafada da sauran kasashen duniya.

A cewar tasa, bayar da damar tattara sakamakon zaben da hannu, zai iya bayar da damar yin magudin zabe a lokacin zaben.

Ya ce, “Ya kamata a ce Nijeriya tana samun ci gaba ta fuskar gudanar da zabukanmu, ba wai kullum sai samun koma baya ba.”

Kazalika, Farfesa Eric Adagbata, ya yi Allah wadai da tattara sakamakon zaben da hannu.

Yana mai cewa, bai kamata majalisar tarayya ta yi la’akari da shi a wannan lokaci ba.

A wurinsa, kamata ya yi a ce Nijeriya tana samun ci gaba, ba wai kuma ci baya ba, ya kara da cewa; yaya za a ce, kasar ba za ta iya samar da abin da ake bukata a 2027 ba.

Wani Lauya, Igene A. Amos, ya yi kira da a yi hattara, inda ya kara da cewa; kasar ba ta kai matakin da za ta iya watsa sakamakon zabe ta hanyar na’urar ba.

Ya ci gaba da cewa, tattara sakamakon zaben da hannu kuma zai kara karfafa magudin zabe, amma ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ta kuma tabbatar da cewa; ba a yi magudin a lokutan zabee ba.

Dakta Wahab Shittu (SAN), ya yi gargadin cewa; amincewar majalisar dattawan, na iya yin kasadar “kutsawa majalisa cikin wuraren da kundin tsarin mulki ya kayyade,” idan ta iyakance ikon da hukumar INEC take da shi.

Wani lauya, Farfesa Ernest Ojukwu (SAN), ya bayyana amincewar majalisar dattijan, ta hanyoyin watsa sakamakon zaben ta na’ura da kuma tattarawa da hannu a matsayin wani abu mai kama da maslaha.

Ojukwu ya ce, “A bangare guda kuma, ana nufin samar da wani tsari, musamman idan aka samu matsala da bangaren na’ura ko kuma kalubale a wannan hanya ta sadarwa, domin tabbatar da ganin cewa; tsarin zabe bai samu nakasu ba, sai a yi amfani da hanyar tattarawa da hannu.

Har ila yau, watsa sakamakon zabe ta hanyar na’ura zuwa tashar hukumar INEC, na nufin kara bayyana gaskiya tare da bai wa ‘yan kasa damar bin diddigin zabukan da suka yi cikin sauki, wanda rashin watsawar ko yaya na iya lalata wannan buri da ake da shi.

Kungiyoyin Farar Hula Sun Yi Fatali Da Matsayar Da Majalisar Dattijai Ta Cimma

Kungiyoyin farar hula (CSOs), da suka hada da Yiaga Africa, Cibiyar Bayar da Shawarar Dokoki (CISLAC), Kungiyar Kula da Rinjaye, Transparency International da kuma Cibiyar Dimokiradiyya da Ci Gaba (CDD ta Yammacin Afirka), sun yi fatali da amincewar Majalisar Dattijai, na amincewa da watsawa ta hanyar na’ura da kuma tattara sakamakon zabe da hannu.

Majalisar dattijan, a ranar Talata ta amince da aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura zuwa tashar duba sakamakon zabe ta hukumar INEC, yayin da ta ba da damar kuma tattarawa da hannu a lokacin da na’urar watsawar ta gaza.

Sai dai, babban daraktan na Yiaga Africa, Samson Itodo, ya ce; sharuddan da ke cikin wannan sashe, na nuni da samun koma baya a zaben da kuma raunana matakan kariya na dokar zabe ta 2022.

Ya shaida wa LEADERSHIP cewa, gaza yin amfani da na’ura wajen watsa sakamakon zaben, na iya lalata ingancin zaben kwata-kwata.

A nasa bangaren, babban daraktan kungiyar (CISLAC), kuma shugaban kungiyar sa ido kan canjin yanayi da kuma ‘Transparency International’, Auwal Musa-Rafsanjani, ya ce; majalisar dattawan, ta yi nasarar samar da yanayin magudi da rashin gaskiya a lokutan zabe.

“Abin da majalisar dattijai ta yi, don samun nasarar yiwuwar magudin zabe ne kadai, wato ta hanyar karfafa ci gaba da tattara sakamakon zabe da hannu.”

Ga babban daraktan CDD-West Africa, Dakta Gauda Garuba kuma, ya kalli al’amarin a matsayin matakin da majalisar ta dauka na nuni da yi wa ‘yan Nijeriya juyin mulki ne.

“Na kalli zaman majalisar dattijai kai tsaye, a gidan talabijin na Channels, a yayin da ake nazarin kudurin, Majalisar koli ta hanyar yin magudi a fili na shugabancinta, ta aiwatar da juyin mulki ga ‘yan Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *