Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC

[ad_1]


Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce bai sha wahala ba wajen yanke shawarar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC ba, yana mai bayyana matakin a matsayin zabi mai sauƙi a rayuwar siyasarsa.

Fubara ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake zantawa da ’yan jarida a shalkwatar APC ta ƙasa, inda ya ce ya dade yana jin kansa a waje a cikin PDP, musamman a lokacin rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Ribas. A cewarsa, shiga APC wata hanya ce ta nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu da kuma haɗa kai don ci gaba da bunƙasa jihar da ƙasa baki ɗaya.

“Gaskiya idan zan faɗi ra’ayina, ban taɓa jin kaina cikakken ɗan PDP ba,” in ji Fubara. “A lokacin rikicin, ban kasance cikin wata ƙungiya ba. Ina kallon abubuwa ne daga waje, kamar mutum da ke tsaye a baranda.”

Sauya shekar gwamnan ya biyo bayan dogon rikici tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, kan iko da tsarin jam’iyyar PDP a jihar. Rikicin ya kai ga Shugaba Tinubu dakatar da gwamnan, da mataimakinsa da Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida kafin daga bisani a dawo da su bakin aiki.

Bayan dawowarsa aiki a watan Satumba, Fubara ya sanar da shiga APC a ranar 9 ga Disamba, 2025, matakin da ake ganin yana da muhimmanci gabanin zaɓen 2027. Gwamnan ya ce a matsayinsa na “mai kishin ci gaba,” zai haɗa kan ’yan APC a Ribas tare da samar da sabon shugabanci mai alkibla a jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *