’Yan bindiga sun ƙaƙaba wa manoman rake haraji a Kano da Katsina

[ad_1]



Ana zargin wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga masu ɗauke da makamai da ke addabar wasu sassan jihohin Katsina da Kano da ƙaƙaba harajin naira dubu 50 kan kowace hek­ta ga manoman rake kafin su yi girbi.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kafa irin nasu tsarin iko a wasu yankunan dazuzzuka, inda suke tilasta wa manoma biyan haraji kafin su girbe amfanin gonakinsu.

A cewar bayanan da ke fitowa daga yankunan da abin ya shafa, ’yan bindigar sun bazu a cikin Dajin Rugu da ke ƙaramar hukumar Safana, wanda ya haɗa har zuwa yankin Faskari a Jihar Katsina, da kuma Dajin Falgore da ke ƙaramar hukumar Doguwa a Jihar Kano.

A waɗannan yankuna, suna karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba tare da yin barazana ga manoman da suka ƙi bin umarninsu, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Rahotannin sun ce manoman da suka ƙi biyan harajin na fuskantar barazanar lalata amfanin gonakinsu, ko kai musu hare-hare masu tsanani, lamarin da ya tilasta wa da dama barin gonakinsu baki ɗaya.

Ko da yake manoman rake ne suka fi fuskantar wannan matsin lamba, rahotannin sun nuna cewa manoman masara ma ba su tsira daga wannan hali ba.

Wani mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, da aka fi sani da Bakatsine, ya bayyana a shafinsa na X (@DanKatsina50) cewa dazuzzukan da abin ya shafa na daga cikin manyan yankunan noman abinci a jihohin Katsina da Kano.

A cewarsa, yankunan su ne manyan hanyoyin samar da rake da masara a kasuwanni kamar Dandume da Mai’aduwa a Jihar Katsina, da kuma kasuwar Dawanau da ke Jihar Kano.

Masana harkar noma sun yi gargaɗin cewa ci gaba da kawo cikas ga ayyukan noma a yankin na iya haifar da ƙarancin abinci da hauhawar farashi a faɗin Arewacin Najeriya.

Duk da kasancewar wuraren binciken sojoji da ’yan sanda a kan titin Falgore, rahoton ya yi nuni da cewa ’yan bindigar na gudanar da ayyukansu ne a wuraren da ba su wuce kilomita biyar daga wuraren tsaron ba.

Mazauna yankunan da al’ummomin manoma sun bayyana lamarin a matsayin ƙwace iko a hankali, inda ’yan bindigar ke kafa dokokinsu, karɓar haraji, da kuma mallakar ayyukan tattalin arziƙi na yau da kullum ba tare da wata turjiya ba.

Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatocin jihohin Katsina da Kano ko hukumomin tsaro dangane da wannan zargi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *