Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin shugaban kasa, Bola Tinubu, na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da zaman lafiyar mashigin tekun Guinea, musamman sauye-sauyen da ake yi a hukumar da ke kula da mashigin tekun Guinea (GGC).
Ya kuma jaddada himmar Nijeriya wajen yin hadin gwiwa a yankin da kuma cika alkawuran tsarin kula da teku na shekarar 2050 da kungiyar hadin kan Afrika ta shirya.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar, mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin babban sakataren GGC, Mista Jose Mba Abeso, da tawagarsa a wata ziyarar ban girma da suka kai fadar shugaban kasa a Abuja.
“A madadin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ina kara tabbatar da tsayin dakar Nijeriya ga manufofin GGC. Babu wanda zai iya gurgunta rawar da hukumar ke takawa wajen samar da hadin kai, zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa a mashigin tekun Guinea,” in ji shi.
Ya yaba wa mahukuntan GGC, yana mai ba su tabbacin cewa, “Nijeriya na nan tsayin daka kan kare manufofin hukumar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Yayin da tutoci suka rika kadawa, kade-kade na tsuma maza suka rika tashi, kusan ko ina ya cika da batun tarihi a titunan birnin Beijing, ba sai an fada ba sakon ya fito fili karara, wato jama’ar kasar Sin na tunawa da samun nasararsu a kan kare martabar kasa daga zaluncin mamayar dakarun Japanawa.
Yau Laraba, 3 ga watan Satumba, rana ce ta cika shekaru 80 da samun wani muhimmin lokaci a tarihin zamani da ya kunshi manyan abubuwa biyu, na farko nasarar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa, da kuma babbar nasarar da sojojin kawance suka samu a yaki da mulkin danniya a duniya wanda aka fi sani da Yakin Duniya Na Biyu.
Gagarumin bikin ranar da aka yi yau a kasar Sin ba wai kawai na tunawa da nasarar soja ba ne, girmamawa ce ga tsayin daka, sadaukarwa, da hadin kan al’ummar da ta yi fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru 14. Tun daga abin da ya faru a ranar 18 ga Satumba a shekarar 1931 (na kaddamar da hare-hare) zuwa mika wuyar kasar Japan a shekarar 1945, kasar Sin ta yi gwagwarmayar tsira da mutuncinta daga mamayar zalunci har ta kai ga asarar rayukan sojoji da fararen hula fiye da miliyan 35. Kuma duk da shiga cikin tsananin wahalhalu da ba za a iya misaltawa ba, jama’ar kasar Sin sun tsaya tsayin daka, tare da ba da gudummawa sosai ga fatattakar ‘yan mulkin danniya a duniya.
Gadon tsayin dakar da jama’ar kasar Sin suka yi shi ne ya zama ruhin kasar, ya kuma ba da gudunmawa ga haifar da sabon tsari na duniya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, tare da sadaukar da kai ga zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya. Sai dai kuma, a yayin da tashe-tashen hankula a duniya ke kara ta’azzara a zamanin nan kuma masu ba da labarin abin da ya faru suka fara gurbata hakikanin tarihi, rawar da kasar Sin ke takawa wajen kare gaskiyar lamarin na da matukar muhimmanci.
Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a taron Tianjin na Kungiyar Hadin Gwiwar Shanghai (SCO), ya sake jaddada aniyar kasar Sin wajen raya mu’amala da bangarori daban daban, da daidaiton ‘yancin kasashe, da hadin gwiwar duniya baki daya. Gabatar da shawarar Tsarin Shugabancin Duniya (GGI) ta nuna sabon kokari na kiyaye kyawawan ka’idojin da aka kafa bayan yakin duniya na biyu domin ci gaban kasa da kasa.
Kazalika, wannan biki na tunawa da nasarar fatattakar zalunci yana tunatar da mu mahimmancin waiwaye a kan tarihi. Fina-finai da aka yi game da hakan kamar “Dead to Rights”, da bikin nune-nunen a sassan yankin Macao, da faretin soja a birnin Beijing, hidindimu ne na sake duba tarihi, da sadaukarwar al’ummomin da suka gabata domin ci gaba da zaburar da na yanzu da wadanda za su zo gaba.
Birnin Beijing ya cika da annashuwa da alfahari yayin da dandalin Tian’anmen ya shaida gagarumin faretin soji domin bikin na yau. An yi gaisuwar ban-girma ta hanyar harba bindigogi 80 a sassan babban birnin domin karrama mazan jiya da suka kwanta dama da kuma wadanda suke raye. Sojoji sun yi tattaki cikin tsari mai kyau, jiragen sama sun yi fenti mai launin ja da zinariya a sararin sama, kuma tsoffin sojoji da suka halarci bikin sun kasance a matsayin shaida na jajircewa.
Shagulgulan al’adu da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin da aka watsa a sassan kasar har ma da duniya baki daya sun kara raya ruhin tunawa da wannan nasara a cikin gidaje da zukatan jama’a a fadin kasar da sauran abokai na kasa da kasa. Yanayin yau a kasar Sin ya kasance na biki mai matukar armashi da ke kara girman kishin kasa tare da girmamawa ga sadaukarwar da aka yi shekaru 80 da suka gabata.
Darussan wannan tarihi a bayyane suke, wato hadin kai wajen fuskantar zalunci da kuma kiyaye mutunci domin tabbatar da adalci a doron kasa kuma tabbas, kasar Sin ta nuna gado mai kyau ta wannan fuska. Don haka, ya kamata wannan rana ta zama ba lokacin tunani ne kawai a kan nasarar da aka samu ba, amma a kan abin da ya zama wajibi a kiyaye shi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shugaba Bola Tinubu, ya ce kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga hanyoyin da ba na man fetur ba sun isa wajen daƙile tasirin manufofin tattalin arziƙin shugaban Amurka, Donald Trump.
Trump, ya sanya sabbin dokoki, ciki har da haraji masu tsauri, wanda suka jawo suka daga sassa daban-daban na duniya.
Yayin da yake karɓar tawagar ‘The Buhari Organisation’ ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Almakura, a fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce Najeriya ta riga ta cimma burin samun kuɗaɗenta na shekarar 2024 tun daga watan Agusta.
“Mun riga mun cimma burin samun kuɗin shiga na wannan shekara tun a watan Agusta.
“Kuɗaɗen da ba na man fetur ba ne, ba ma jin tsoron abin da Trump yake yi a can,” in ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta daidaita tattalin arzikin ƙasa tare da rage dogaro da man fetur, don haka matsin lamba daga waje ba zai hana ci gaba da samum kuɗaɗen ƙasar ba.
Trump ya sha kiran ƙungiyar OPEC da ta ƙara fitar da adadin mai domin rage farashinsa a duniya.
A watan Yuli, OPEC da abokan haɗin gwiwarta sun amince da ƙara samar da ganga dubu 548 a kowace rana daga watan Agusta.
A watan Afrilu kuma, Trump ya sanya wa ƙasadhe haraji, ciki har da kaso 14 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya.
Bayan haka ya sanya hannu kan dokar dakatar da rangwamen haraji ga ƙasashe a ƙarƙashin dokar gaggawa ta tattalin arziƙin Amurka.
A shekarar 2023, Najeriya ta fitar da kaya zuwa Amurka da suka kai dala biliyan 6.29.
Daga Cikinsu akwai man fetur mai na dala biliyan 4.73, gas dala miliyan 920, da takin zamani dala miliyan 167.
Wata kungiyar rajin kare dimokuradiyya, mai kare shirin sabunta fata na shugaba Tinubu (the Renewed Hope Interest Defenders), a ranar Laraba, ta yi na’am da shirye-shiryen sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, farfado da matatun mai na cikin gida, dokokin da aka zartar da nufin bunkasa zuba jari a bangaren mai da iskar gas.
Sai dai kungiyar ta bukaci a gaggauta dakatar da shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari.
Shugaban kungiyar, Obed Agu, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce, zaman bitar ayyuka zango na uku ya nuna cewa manufofin Tinubu na da “nufin samar da ci gaba mai dorewa ta hanyar samar da mai mai rahusa, sauke farashin kayayyaki da kuma kyakkyawan fatan samun daidaiton tattalin arziki.”
Sai dai ya zargi shugaban na NNPCL da shirin zagon-kasa kan duk wannan kyawawan manufofin na Tinubu.
A cewar kungiyar, Ojulari ya yi watsi da tattaunawa kan wani rancen dala biliyan 5 na kasar Saudiyya da shugaban kasa ya lalubo a watan Nuwamba 2023, domin ci gaba da aikin gyaran matatar mai ta Fatakwal duk da cewa tana aiki da kashi 60 cikin 100.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
A yau, al’ummar kasar Sin sun gudanar da wani gagarumin gangami da faretin soji a birnin Beijing na kasar, domin tunawa da cikar shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Shugabanin wasu kasashe 26 ne suka halarci bikin tunawa da ya gudana, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin cewa, jama’ar kasar Sin za su tsaya tsayin daka wajen bin tafarki na gaskiya, wanda zai haifar da ci gaban daukacin dan Adam, da bin hanyar raya kasa cikin lumana, da yin aiki kafada da kafada da al’ummun kasashe daban daban, wajen gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama.
Me ya sa Sinawa za su iya bin tafarki na gaskiya? Domin sun dade suna jin radadin yake-yake.
Kasar Sin babban fagen daga ne a yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Lokacin da sojojin Japan suka fara mamaye kasar Sin a shekara ta 1931, Sinawa sun kasance na farko a duniya wajen daga tutar yaki da tafarkin murdiya. Yayin da wasu kasashen yammacin duniya ke tunanin magance yaki da ‘yan Nazi, sojoji da fararen hula na kasar Sin sun riga sun tashi haikan don yaki da maharan kasar Japan, ko da yake ba su da makamai masu inganci a lokacin.
Sama da shekaru 80 da suka gabata, kasar Sin ta kasance cikin talauci da rauni, kuma sadaukarwar da Sinawa suka yi wajen kare kasarsu tana da yawa. Bisa kididdigar da aka yi, yawan sojojin kasar Sin da fararen hula na kasar da suka rasa rayuka, ko kuma suka ji rauni a yakin da suka yi da sojojin Japan ya zarce miliyan 35, inda yawan hasarar da aka samu ya haura dala biliyan 600. Al’ummar kasar Sin, bisa babbar sadaukarwar da suka yi, sun samar da damar cin nasara a yakin da jama’ar kasashe daban daban suka yi na kin tafarkin murdiya. Saboda a yayin yakin na tsawon shekaru 14 da Sinawa suka yi da maharan kasar Japan, fagen daga dake kasar Sin ya janyo hankalin kaso 60% zuwa 94% na sojojin kasa na kasar Japan. Wannan yanayi ya wargaza muradin sojojin Japan da masu bin tafarkin murdiya na kasar Jamus, na hadin gwiwa a kokarin mamaye duniya daga dukkan bangarorin gabas da yamma.
Yakin da Sinawa suka yi cikin adalci ya sa su samun karramawa, da goyon baya daga gamayyar kasa da kasa. Kana yadda al’ummun kasashe daban daban a wancan lokaci suka hada kai da juna a karkashin tutar yaki da tafarkin murdiya, ko da yake akwai bambanci a tsakaninsu ta fuskokin kasa, da kabila, da kuma akida, ya kai ga cimma nasara a yakin kin tafarkin murdiya, da tabbatar da sabon tsarin kasa da kasa bayan yakin a karshe.
Tarihin yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya ya nuna mana wasu tunani masu zurfi, wadanda jama’ar kasar Sin suka san su sosai:
Da farko dai, komai wahalhalun da aka sha, adalci zai yi galaba a kan muguntawa, haske kuma zai kori duhu. Wannan tamkar doka ce ta tarihi.
Na biyu, ‘yan Adam na da makomar bai daya. Ya kamata a samu daidaituwa, da jituwa, da cude-ni-in-cude-ka, tsakanin kasashe da kabilu daban daban, ta yadda za a samu damar tabbatar da tsaron bai daya, da kawar da yaki daga karshensa.
A zamanin da muke ciki, ana ta samun abkuwar rikice-rikice a duniya, inda dan Adam suka sake fuskantar bukatar yin zabi tsakanin cudanya da juna ko yin gaba da juna, zaman lafiya ko yaki. Sai dai kasar Sin ta riga ta samu babban ci gaba: Yanzu kasar na bikin tunawa da nasarar da ta samu ta gagarumin faretin soji. Kana a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jama’ar kasar na ta kokarin zamanantar da kasarsu bisa hadin kansu.
Jawabin shugaba Xi Jinping ya bayyanawa duniya cewa: Kasar Sin mai karfi za ta ci gaba da samar da gudummawa ga ci gaban al’ummar dan Adam da na tattalin arzikin duniya cikin lumana.
Bari mu yi kokarin neman samun ci gaba tare, bisa wani tafarki na gaskiya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ba daidai ba ne a riƙa cewa Boko Haram Kiristoci kawai suke kashewa a Arewa maso Gabas.
Ya bayyana cewa ƙungiyar tana kai wa Musulmi da Kiristoci hare-hare baki ɗaya, don haka bai kamata a alaƙanta ta da addini ɗaya ba.
Ndume, ya mayar da martani ne kan wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa wanda ta yi iƙirarin cewa dukkanin waɗanda aka kashe kwanan nan a hare-haren Boko Haram Kiristoci ne.
Ya ce a hare-haren da suka faru a ƙarshen mako a Jihar Borno, Musulmi biyar aka kashe a ƙauyen Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a ranar Asabar.
Sannan an kashe Kiristoci uku a ƙauyen Mussa na Karamar Hukumar Askira-Uba a ranar Lahadi.
Sanatan ya yi gargaɗin cewa yaɗa irin wannan labari yana da hatsari domin yana iya raba kan jama’a, yana rage wa sojojin da ke yaƙi da ta’addanci ƙwarin guiwa, kuma ya iya kawo mummunan sakamako.
Ya ce Boko Haram ba sa kallon addini ko ƙabila, domin kai wa talakawa hare-harensu, waɗanda kawai suke neman zaman lafiya da yin noma.
Ndume ya yaba wa sojoji bisa jajircewarsu wajen yaƙi da ’yan ta’addan, amma ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara kula da walwalar sojojin tare da samar musu da isassun makamai domin su samu damar yaƙar Boko Haram.
Jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Farouk Adamu Aliyu, ya ce shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓe a shekarar 2027.
Yayin hira da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Aliyu ya ce jam’iyyun adawa ba su da ƙarfi, ya kuma nuna tabbacin cewa Tinubu zai dawowa kan mulki.
Ya ce shugabanci yana da ƙalubale, inda ya zargi mutane da jingina duk matsalolin ƙasar kan shugaban ƙasa.
A cewarsa, wasu daga cikin sukar da aka yi wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a lokacin mulkinsa ba su dace ba.
Aliyu ya jaddada cewa: “Babu abin da zai hana Shugaba Bola Tinubu ya dawo a 2027.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce da a ce yana da cikakken iko da jami’an tsaro, da zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar shi a cikin mako biyu.
Gwamnan ya kuma ce ya san dukkan inda ’yan bindigar jihar suke buya.
Da yake jawabi a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce babban kalubalen shi a yaki da ’yan bindiga a jihar shi ne rashin cikakken iko da jami’an tsaro. ya ce shugabannin rundunonin tsaron da ke jihar suna karbar umarni ne kawai daga hedkwatocinsu da ke Abuja, bad aga wajen shi ba.
A cewar Gwamnan, “Na rantse da Allah na san duk inda wani shugaban ’yan bindiga yake a Zamfara, kuma duk inda ya fita ya je na sani.
“Yanzu da wayata zan iya nuna muku inda wadannan ’yan ta’addan suke a yau. Amma babu abin da za mu iya yi musu.
“Wallahi a yau da ina da iko da jami’an tsaro, ina mai tabbatar maka za mu iya kawo karshen ’yan bindiga a Zamfara cikin wata biyu.
“a lokuta da dama nakan zubar da hawaye ga mutanena ganin yadda matsalar take, amma ba ni da ikon da zan ba jami’an tsaro umarni su yi maganinta.
“Akwai lokacin da ’yan ta’adda suka taba kai hari karamar hukumar Shinkafi, kuma ina zaune a nan lokacin da aka ankarar da jami’an tsaro, amma suka ki zuwa saboda wai ba a ba su umarni daga Abuja ba. Wannan ce babbar matsalar da muka fuskanta, amma mun dogara ga Allah, zai kawo mana mafita.”
Gwamna Lawal ya ce amma duk da haka, gwamnatin jihar na ba jami’an tsaro tallafin kayan aiki da kudaden gudanarwa na yau da kullum, inda ya ce bayanan hakan na nan ga duk mai bukata.
Ya kuma ce ko a wata biyu da suka gabata, gwamnatin jihar ta raba motocin sintiri guda 150 ga jami’an tsaro na sojoji, ’yan sanda da DSS da kuma sibil difens domin su inganta ayyukansu.
Gwamnan ya kuma ce ya dauko hayar mafarauta sama da 2,000 daga jihohin Borno da Yobezuwa jihar domin tallafa wa kokarin jihar na yaki da ’yan fashin dajin.
Jama’ar gari sun kone wani mutum da ake zargi da satar babur da safiyar Talata a kan titin Ibrahim Kashim Road da ke Makurdi, babban birnin jihar.
Wani ganau da ya ce sunansa Andrewa Tergu, ya shaida wa wakilinmu cewa fasinjoji biyu ne suka hau kan babur din wani dan acaba da nufin ya kai su unguwar Railway Quarters a garin na Makurdi.
Sai dai dan acabar bai sani ba, ashe akwai wani mutum daya da yake tsaye a daidai inda zai sauke fasinjojin, inda yake tsaye yana jiran su isa.
Da isar su, sai ya sa hannun a aljihu kamar zai ciro kudi ya sallami dan acabar, amma sai ya zaro almakashi ya caccaka masa a wurare daban-daban.
Andrew ya ce dan acabar ya fado daga kan babur din nasa inda ya rika ihun neman taimakon mutanen gari.
“A kokarin barayin na guduwa ne daya daga cikinsu ya fado daga kan babur din da suka sata, inda mutane suka far masa da duka, suka jawo shi kan titi sannan suka banka masa wuta,” in ji Andrew.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, lokacin da wakilinmu ya ziyarci inda wurin ya faru, ya iske jami’an Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar suna kokarin share wurin da aka kone wanda ake zargi da satar babur din.
Da muka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta yi alkawarin ba wakilinmu cikakken bayani daga bisani.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba ta kai ga yin hakan ba.