Category: Latest News

  • An Fara Bincike Kan Ɓarkewar Kwalara A Sokoto – Kwamishina

    [ad_1]

    Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da ɓullar cutar cholera a garin Tureta, ƙaramar hukumar Tureta, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

    Kwamishinan lafiya na jihar ya ce an tura samfurin majinyatan zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ke Jihar Oyo domin tabbatar da cutar. Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da magunguna ƙyauta tare da taimakon likitoci, inda ya bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa suna amsawa da magani.

    Sai dai, mazauna yankin sun yi iƙirarin cewa aƙalla mutane goma ne ke mutuwa a kullum sakamakon annobar, duk da cewa hukumomin lafiya sun rage muhimmancin wannan kididdiga, suna mai cewa har yanzu ana kan bincike kan ainihin dalili da kuma yawan waɗanda abin ya shafa.

    Rahotanni sun nuna cewa mata, da ƙananan yara da ƴan gudun hijira ne suka fi kamuwa da cutar. Masana sun alaƙanta ɓullar cutar da yawan mutanen da suka tsere daga hare-haren ƴan bindiga, wadanda yanzu ke cunkushe a makarantu, da kasuwanni da rumfunan kan hanyoyi ba tare da wadatattun wuraren tsafta da kiwon lafiya ba.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’

    [ad_1]



    Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14 daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.

    Cibiyar Gargaɗi Kan Ambaliya (FEWS) ta ma’aikatar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

    Sanarwar, wacce Daraktan Kula da Zaizayar Ƙasa da Ambaliya na ma’aikatar ya fitar, ta gargadi dukkan masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye domin kare kansu.

    A cewar sanarwar, garuruwan da jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Kuros Riba (Edor, Ikom, Itigidi, Akpap), Kano (Gwarzo, Karaye), Zamfara (Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukuyum), Taraba (Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gembu, Gun Gun Bodel, Kambari, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Bandawa, Ngaruwa), Abia (Eziama, Umuahia) da kuma jihar Yobe (Geidam, Kanama, Potiskum).

    Sauran wuraren sun haɗa da jihar Filato (Langtang, Shendam, Wase), Borno (Ngala), Imo (Okigwe, Otoko) Neja (Sarkin Pawa), Sakkwato (Sakkwato, Wamakko, Isa, Shagari, Makira), Kaduna (Kafanchan) da kuma Akwa Ibom (Oron).

    Daga nan sai ma’aikatar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati da su kasance cikin shiri.


    [ad_2]

    Source link

  • Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda

    [ad_1]



    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta yi gargadin cewa sabon salon da ’yan mata suka fito da shi na karbar kudin samarinsu da nufin za su je wajensu amma su ki zuwa laifi ne da za a iya hukunta su da shi.

    A cikin wani bidiyo da Kakakin rundunar a jihar, Grace Iringe-Koko, ta wallafa ranar Laraba, ta ce yin hakan daidai yake da da damfara, kuma za a iya hukunta duk wacce ta aikata.

    A cewar kakakin, “Me ya sa za ki karbi kudi daga wajen mutum kuma ki ki zuwa wajensa, hakan laifi ne da mai aikata shi zai iya fuskantar hukunci.

    “Yin hakan hukuncinsu daya da mallakar kudade ta hanyar yaudara wanda ake kira da 419,” in ji Grace.

    Kakakin ta kuma ce yin hakan daidai yake da aikata laifin zamba cikin aminci wanda idan wanda aka yi wa laifin ya kai kara za a iya hukunta wacce ta aikata.

    Daga nan sai ta yi kira ga sauran jama’a da su guji damfarar mutane ta hanyar saba alkawari.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Kebbi Ta Ba Da Ƙwangilar Gina Hanyoyi Kan Naira Biliyan 2.1

    Gwamnatin Kebbi Ta Ba Da Ƙwangilar Gina Hanyoyi Kan Naira Biliyan 2.1

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da ƙwangilar shimfiɗa hanyoyi guda huɗu a yankin Barikin Mopol da ke Badariya, Birnin Kebbi, kan kuɗin Naira biliyan 2.174 ga kamfanin B-TECH Global Services Ltd. An sanya hannu kan yarjejeniyar kwangilar a ofishin Kwamishinan Ayyuka na jihar, Hon. Abdullahi Umar Faruk Muslim.

    Kwamishinan ya bayyana cewa aikin zai haɗa da shimfiɗa tituna da kuma magudanan ruwa domin gujewa ambaliyar ruwa. Ya ce wannan wani ɓangare ne na shirin Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu wajen samar da ci gaba ga al’ummar jihar, musamman mazauna unguwar Badariya wadda ke da yawan jama’a.

    A cewarsa, za a gudanar da aikin cikin watanni 18 tare da sanya ido daga injiniyoyin gwamnati domin tabbatar da inganci. Haka kuma ya gargaɗi kamfanin da kada ya kuskura ya yi aiki maras kyau, yana mai jaddada cewa gwamnati ta tanadi ƙa’ida wacce ke wajabta kamfani ya kula da aikin tsawon shekara guda kafin a miƙa shi ga gwamnati.

    Gwamnatin

    An bayyana cewa za a biya kamfanin kashi 40% na kuɗin kwangilar a matsayin kuɗin farko domin fara aiki. Wakilin kamfanin, Bashar Shamaki, ya tabbatar da cewa za su fara kawo kayan aiki cikin sati biyu tare da gudanar da aiki mai inganci, yana mai gode wa gwamnatin jihar bisa wannan amincewa.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa

    NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa

    [ad_1]



    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kashe ’yan ta’adda sama da 15 a wani harin jiragen yaƙi da ta kai dajin Sambisa, da ke Jihar Borno.

    Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya ce an ƙaddamar da harin ne a ranar Laraba karkashin Operation Haɗin Kai.

    Ya ce sun samu bayanan sirri da suka nuna cewa mayaƙan da ke da hannu a hare-haren a yankin Bitta sun ɓuya a wajen.

    Ya ce hare-haren sun lalata maɓoyar ’yan ta’addan tare da raunata da dama da cikinsu.

    Ejodame ya ƙara da cewa wannan ya nuna ƙwarewar NAF da kuma jajircewarta wajen tallafa wa sojojin ƙasa da kare rayukan ’yan Najeriya.

    “Duk nasarar da ake samu tana ƙara kusantar da Najeriya wajen samun zaman lafiya ta hanyar rushe hanyar sadarwar ’yan ta’adda,” in ji shi.

    Hakazalika, a farkon makon nan dakarun Operation Haɗin Kai tare da tallafin sojin sama sun kashe ’yan ta’adda 20 a Jihar Borno da Yobe.

    Har ila yau, sun kama wasu da ke taimaka musu da kuma lalata wasu bama-bamai da suka samu a wajensu.


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu Zai Ƙaddamar Da Masana’antar Battirin Lithium A Nasarawa

    [ad_1]

    Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyara Jihar Nasarawa a wannan wata domin kaddamar da sabon kamfanin sarrafa battirin lithium.

    Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja. Ya ce kamfanin, wanda ‘yan kasuwa daga kasar Sin suka gina a karamar hukumar Nasarawa, ya fi girma sau biyu kan wanda aka bude a shekarar 2023, wanda ke da ikon sarrafa ton 3,000 na albarkatun lithium.

    A cewar Gwamna Sule, shugaban kasa zai kaddamar da wannan masana’anta ne bayan dawowarsa daga hutun makonni biyu da yake yi a kasar Faransa.

    Ya bayyana cewa aikin na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na dakatar da fitar da albarkatun kasa ba tare da sarrafa su a cikin gida ba, tare da bunkasa masana’antu a cikin kasa.

    Sule ya kuma ce gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta yi, musamman cire tallafin man fetur da hada tsarin musayar kudin kasa, sun karawa jihohi kudi tare da jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Umar FK ya fice daga PDP zuwa APC da magoya bayansa a Gombe

    [ad_1]



    Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC.

    FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta.

    Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa.

    “Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK.

    Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara wa gwamnan baya a shirin neman kujerar Sanatan Gombe Arewa a 2027.

    Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, da shugaban APC a Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abubakar Danladi, sun tarbi FK cikin farin ciki, inda suka ce dawowarsa babbar nasara ce da za ta ƙara APC ƙarfi a jihar.


    [ad_2]

    Source link

  • Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin

    [ad_1]

    Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya damuwa da maganganun ‘yan siyasar Arewa da ke ayyana niyyar ƙalubalantar shi a zaɓen 2027, duba da yadda yankin Arewa ya kasa dunkulewa wuri guda.

    Jibrin, wanda ke wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a shirin Siyasa a yau na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Laraba. Ya ce, “Abin da muka saba yi shi ne, idan wani ya taso daga Arewa, sai mu haɗu mu rusa shi. Wannan shi ake yi. Kuma ina tabbatar maka, waɗanda suke cewa za su tsaya takara su kayar da Bola Tinubu, shi kuwa yana murna ne saboda yana ganin yadda muke cikin rikici da rarrabuwar kai. “

    Ya tunatar da yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya samu saɓani da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, sakamakon adawar da wasu ƴan Arewa suka yi masa wajen neman ƙarfafa tushen siyasa. Haka kuma ya ambaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo da mai ci yanzu, Kashim Shettima, da su ma suka taɓa fuskantar irin wannan matsin lamba daga yankin Arewa.

    Jibrin ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa suka fara ɗaukar zafi kafin 2027, inda batun rabon mulki (zoning) da neman haɗin kai ke ci gaba da jan hankali a fafutukar neman shugabanci.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa

    [ad_1]



    Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, dan Majalisar Wakilan Najeriya ya ce jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a shirye yake ya tattauna da jam’iyyar APC kan batun komawa cikinta.

    Dan majalisar, wanda makusancin Kwankwason ne dai a ’yan makonnin da suka gabata sau biyu yana ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja a kan batun Kwankwason.

    Kofa ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a shirinsu mai suna Siyasa a yau ranar Laraba.

    Sai dai Kofa wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar ya ce ya ce wasu daga cikin ’yan jam’iyyar ta APC a jiharsu ta Kano ba za su so komawar tsohon Gwamnan na Kano ba.

    Amma ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa a kan batun.

    Ya ce, “Idan ka ce Kwankwaso zai koma APC, ko kuma za mu koma APC, hatta a cikin ita APC din a Kano, akwai mutane da yawa da ba za su so ya koma ba, watakila masu son zama Gwamna da ma wadanda ba Gwamnan suke son zama ba.

    “Na yi iya kokarina wajen ganin siyasar Kano da ta Najeriya ta daidaita, amma tana da sarkakiya sosai.

    “Amma kowa ya sani, tun daga farkon wannan gwamnatin, na yi ta fadi-tashin ganin mun yi aiki tare wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa.

    “In dai maganar komawa APC ce, ya sha nanata cewa kofarsa ta tattaunawa a bude take, kofofinmu a bude suke, komai zai iya faruwa,” in ji dan Majalisar.


    [ad_2]

    Source link

  • NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027.

    A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link