Category: Latest News

  • Ya Kamata El-Rufai Ya Yi Bayani Kan Zargin Gwamnati Na Biyan ‘Yan Bindiga Kuɗaɗe

    [ad_1]

    Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Datti Baba-Ahmed, ya ce dole a tambayi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, game da iƙirarin da ya yi cewa Gwamnatin Tarayya na biyan ‘yan bindiga kuɗi.

    Yayin hira da gidan talabijin na Channelsa ranar Talata, Baba-Ahmed ya ce wannan magana babba ce, bai kamata a yi watsi da ita ba.

    Ya kuma soki ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA) saboda ƙin amincewa da zargin.

    A baya, El-Rufai ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya da ta Kaduna suna bai wa ‘yan bindiga kuɗaɗen wata-wata tare da kayan abinci.

    Duk da cewa NSA da gwamnatin Kaduna sun musanta zargin, Baba-Ahmed ya bayyana cewa El-Rufai ya kamata ya yi bayani a gaban jami’an tsaro da kuma kotu.

    Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki.

    A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ’Yan daba sun tarwatsa taron neman zaman lafiya na dattawan Katsina

    [ad_1]



    Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata.

    Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

    Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.

    Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalolin tsaro na ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya yi sanadin kisan mutane da dama tare da rasa dukiyoyi na miliyoyin Naira.

    Sai dai an kai harin ne a daidai lokacin da Gwamnan jihar, Dikko Umar Radda ya jagoranci tawagar dattawan jihar zuwa Fadar Shugaban Kasa Bola Tinubu, inda suka sa labule kan matsalar tsaron jihar.

    Shi dai taron na Katsina ya tattara kwararru da dama, cikinsu har da tsofaffin sojoji da ’yan sanda da malamai da kuma sauran shugabannin al’umma.

    To sai dai an fara samun matsala a taron ne lokacin da wanda ya shirya shi, Dr Bashir Kurfi, ya fara jawabi a kan matsalar tsaron jihar.

    A cikin jawabin nasa dai, ya yi zargin cewa kananan hukumomin jihar da dama yanzu sun kusa zama kufai, yayin da harkokin tattalin arziki da noma da kiwo da ma harkokin karatu suka durkushe saboda hare-haren ’yan bindigar.

    Amma yana cikin jawabi ne sai wani ya tashi ya katse shi, inda ya ce gwamnatin jihar na niya bakinta wajen magance matsalar, amma su ba sag ani, don haka ba za su bar shi ya ci gaba da magana ba.

    Sun kuma zargi Dr Kurfi da cewa dan adawa ne saboda a zamanin gwamnatin da ta gabata bai yi irin wadannan maganganun ba, inda suka kira shi da makiyin gwamnati mai ci.

    Da aka bukaci mai maganar da ya jira lokacin yin tsokaci kafin ya yi bayani, sai wasu takwarorinsa ma suka mike, nan take wajen kuma ya yamutse.

    A nan ne suka fara jifa da kujeru har suna kai wa wasu daga cikin ’yan jaridar da ke daukar rahoto a wajen hari.

    Bayanai sun nuna an girke ’yan dabar a ciki da wajen wurin tarom, yayin da wasu daga cikinsu suka rika nuna wukake suna barazanar caka wa duk wanda suke gani a matsayin makiyin gwamnatin jihar.

    Sai dai duk da harin da ya tarwatsa taron, wanda ya shirya shi ya ce ba za su saduda ba.

    Ya kuma zargi gwamnatin jihar da daukar nauyin ’yan dabar, inda ya ce dukkansu suna da alaka da gwamnatin, domin da bakinsu ma sun fadi hakan.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Hutu

    [ad_1]

    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga watan Satumbar 2025, a matsayin ranar hutu don bikin ranar Mauludin Annabi Muhammad (SAW).

    Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.

    Tunji-Ojo ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin a Nijeriya da sauran sassan duniya, yana mai kira a gare su da su yi koyi da halayen Annabi na zaman lafiya da soyayya da haƙuri da kuma tausayi.

    Ya jaddada cewa irin waɗannan dabi’u ne ginshiƙan gina ƙasa.

    Ministan ya kuma buƙaci ‘yan ƙasar nan, ba tare da la’akari da addini ba, da su yi amfani da wannan dama wajen roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali.

    Ya ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da kula da tsaro tare da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Rungumi Daidaito Da Adalci

    [ad_1]

    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a rungumi akidun tabbatar da daidaito da adalci, tare da tsayawa tsayin daka kan tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, da kara azamar inganta rayuwar al’umma a ko da yaushe.

    Shugaba Xi ya yi kiran ne a yau Laraba, yayin bikin taron tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya.

    Xi ya ce, shekaru 80 da suka shude, bayan shafe shekaru 14 ana gwabza kazamin yaki, al’ummar Sinawa sun yi nasarar murkushe dakarun mamaya na kasar Japan, tare da ayyana cimma cikakkiyar nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan muhimmiyar gaba ta tarihi ta sanya al’ummar kasar Sin ficewa daga zurfin tashin hankali tun shiga zamanin wayewar kai zuwa matakin farfadowar kasa, ya kuma kasance muhimmin lokaci na samun ci gaban duniya. Wannan muhimmiyar nasara ta samu ne ta hanyar hadin gwiwar Sinawa da sauran kawaye masu rajin kin tafarkin murdiya da sauran al’ummun kasashen duniya.

    Shugaba Xi ya kara da cewa, salon zamanantarwa irin na Sin, na kan tafarkin neman ci gaba bisa lumana. Kuma Sin za ta ci gaba da kasancewa babban karfi na wanzar da zaman lafiya, da daidaito da ci gaban duniya. Kana da sahihiyar zuciya, tana fatan dukkanin sassan kasa da kasa za su koyi darasi daga tarihi, za su mutunta hadin kai, tare da hada hannu wajen ingiza zamanantar da duniya da samar da makoma mai haske ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi

    [ad_1]



    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

    Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci.

    Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar.

    Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u da kuma tausayi.

    Tunji ya kuma yi kira ga dukkan ’yan kasar ba tare da la’akari da kowanne irin addini suke bi ba da su yi amfani da lokacin Mauludin wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da tsaro tare da goyon bayan yunkurin gwamnati na bunkasa rayuwarsu.

    “Ministan Harkokin Cikin Gida yana kuma yi wa ’yan Najeriya fatan yin shagulgula cikin farin cikin, natsuwa da kwanciyar hankali,” in jin sanarwar.


    [ad_2]

    Source link

  • Jihohi 18 A Arewa Za Su Iya Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Satumba – NiHSA

    [ad_1]

    Hukumar kula da madatsun ruwa ta Nijeriya (NiHSA), ta gargaɗi cewa wasu jihohi a Arewa cewar za su iya fuskantar ambaliya a makonni biyu na farkon watan Satumba.

    A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce gaba ɗaya jihohi 29 da Babban Birnin Tarayya Abuja ne ke cikin barazanar ambaliya daga 1 zuwa 15 ga watan Satumba.

    Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar ƙananan hukumomi 107, garuruwa 631, da kuma tituna 50 a sassa daban-daban.

    Jihohin da suka fi shiga hatsari sun haɗa da: Borno, Zamfara, Jigawa, Kebbi, Yobe, Filato, Gombe, Taraba da Sakkwato, yayin da a Jihar Kaduna barazanar ba ta da yawa.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Xi Jinping Ya Duba Faretin Rundunonin Sojoji Da Kayayyakin Soja, Shugabannin Kasashe 26 Su Ma Sun Halarci Bikin

    [ad_1]

    Da misalin karfe 9 na safiyar yau Laraba 3 ga Satumba ne aka gudanar da gagarumin bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun Japan, da kuma yakin duniya na kin tafarkin murdiya a filin Tian’anmen na birnin Beijing bisa jigon “Tunawa da tarihi, girmama jarumai, martaba zaman lafiya da kuma samar da ci gaba”, inda aka yi gagarumin bikin faretin sojoji, tare da al’ummomin duniya don tunawa da wannan rana mai girma.

    Cikin sautin wakar soja mai karfi, Xi Jinping dake tsaye cikin wata mota ya bi faffadan titin Chang’an ya duba faretin rundunonin sojoji, da na kayayyakin soja dake jere.

    Yayin wannan biki, akwai rundunoni 45 (da jirage) da aka duba, kuma da farko an duba faretin rundunonin sojoji 13 dake fareti da kafa. Sojojin al’ummar Sinawa sun cimma sabon tsari bayan da aka yi musu kwaskwarima, inda a karon farko aka gabatar da nau’o’in sojoji 4, wato sojin kasa, da sama, da ruwa da roka, da rundunonin sojoji 4, wato sojojin sararin sama, da na yanar gizo, da na tallafin bayanai, da kuma sojoji masu ba da hidima. Ban da wannan kuma, dukkan rundunonin soja da yan sandan tsaron cikin gida, sun rike tutocinsu a wannan biki.

    Bisa goron gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musu, shugabanni 26 na kasashe da na gwamnatocin ketare sun halarci bikin. Sannan wasu shugabannin majalisun dokokin kasashe, da mataimakan firaministocin wasu kasashe, da manyan wakilai, da shugabannin hukumomin kasa da kasa, da tsoffin shugabannin siyasa na kasashe da dama su ma sun halarci bikin.

    Ban da wannan kuma, an gayyaci jakadun ofisoshin jakadanci na kasashen waje dake kasar Sin, da jami’an ofishin jakadanci dake kula da harkokin soji, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa dake zaune a kasar Sin, da abokai 50 da iyalansu daga kasashe 14 da suka hada da Rasha, da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da kuma Kanada.

    Shekaru 80 da suka gabata, al’ummar kasar Sin sun samu gagarumar nasara a yakin kin hare-haren sojojin Japan bayan shekaru 14 masu cike da wahalhalu, tare da bayyana cikakkiyar nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. Sin ta fara yakin kin hare-haren ne tun daga farko har karshe a tsawon lokaci, kuma bisa gagarumar sadaukarwar al’ummun Sin, kasar ta bayar da goyon baya a babban fagen yaki na yaki da mulkin danniya a gabashin duniya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa ga samun nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. (Amina Xu, Safiyah Ma)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • NAFDAC Ta Gano Wasu Jabun Allurai A Kasuwanni, Ta Gargaɗi Jama’a Kan Amfani Da Su

    [ad_1]

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta gargaɗi jama’a kan wasu allurai da ta gano na jabu.

    A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce waɗannan allurai ba su da rajistar NAFDAC, amma ana siyar da su a kasuwanni da shagunan magunguna a sassa daban-daban na ƙasar nan.

    NAFDAC ta ce cikin waɗannan jabun allurai akwai Gold Vision Oxytocin Injection mai ɗauke da lambar rajista ta bogi A4-9566.

    An bayyana cewa an haɗa maganin a wani kamfani da ake kira Anhui Hongye Pharmaceutical Co. Ltd da ke ƙasar China, amma kamfanin Gold Vision Medicals da ke Jihar Enug ke yaɗa shi.

    Hukumar ta roƙi jama’a su guji amfani da irin wannan allura, tare da yin taka-tsantsan wajen sayen magunguna domin kare lafiyarsu.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • DAGA LARABA: Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Wani sabon salo da wannan zamani ya zo da shi shi ne auren gwaji, inda mata kan yi shiga gidan miji da niyyar fita bayan wani lokaci.

    Sai dai manazarta suna cewa hakan ka iya haddasa matsalolin musamman idan mazajen auren ba su san da wannan shirin ba.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu mata suke yin auren gwaji.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP

    [ad_1]

    Gwamnan Jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar ta gaji da rikice-rikicen da wasu ‘yan tsagi ke janyo mata.

    Ya yi wannan magana ne bayan ɓangaren Nyesom Wike ya sanya wasu sharuɗa kafin a gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa.

    Sharuɗan sun haɗa da:

    • Shugaban jam’iyya dole ya fito daga Arewa ta Tsakiya.
    • A sake zaɓen shugabannin jam’iyya a Ebonyi da Anambra.
    • A amince da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calabar.
    • A sake zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Ekiti ba tare da jinkiri ba.

    Sai dai a martaninsa, Bala Mohammed ya ce shugabannin PDP mutane ne da suka san darajar jam’iyya, ba za su bari a riƙa yi musu wasa da hankali ba.

    Ya ƙara da cewa shugaban jam’iyya na ƙasa ya riga ya yi magana a fili, kuma babu wani shakku game da kwamitin da ke shirya taron, domin sun taɓa yin hakan a baya, kuma suna da tabbacin za su yi nasara.

    Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link