Category: Latest News

  • Amurka ta sassauta takunkumin da ta sanya wa man Iran don rage ƙarancin mai a duniya

    [ad_1]



    Amurka ta sassauta takunkumin da ta sanya wa man Iran na ɗan lokaci, domin rage matsalar ƙarancin mai da ake fuskanta a duniya.

    Wannan mataki ya shafi man Iran da aka riga aka loda a cikin jiragen ruwa kafin ranar Juma’a, 20 ga watan Maris.

    An ce sassaucin zai ɗauki tsawon kwanaki 30 ne kacal.

    Sakataren Baitul-malin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen ƙara man fetur a kasuwar duniya, inda ake sa ran za a samu kusan gangar mai miliyan 140.

    An ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya jawo tangarɗa samar da man fetur.

    Masana sun ce wannan sassauci zai taimaka wajen rage tashin farashin mai a kasuwannin duniya, kodayake na ɗan lokaci ne kawai.

    Haka kuma, a baya Amurka ta taɓa sassauta irin wannan takunkumi kan man Rasha da ke kan teku, domin kauce wa matsalar ƙarancin mai.

    Sai dai masana na gargaɗin cewa idan rikicin duniya ya ci gaba, matsalar makamashi na iya dawowa bayan wannan wa’adin ya ƙare.

    Wannan lamari na nuna yadda siyasar duniya da rikice-rikice ke shafar tattalin arziƙi da rayuwar jama’a, musamman a ɓangaren makamashi.


    [ad_2]

    Source link

  • NDLEA Ta Kwace Kwayoyin Pregabalin 75,000 Da Hodar Iblis 556 A Kano

    [ad_1]

    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshen Kano, ta kama kwayoyin Pregabalin guda 75,000, kwalaben maganin tari mai dauke da Codeine 556, da kuma wasu adadin tabar wiwi (Cannabis satiba) a yankin Badawa na Kano.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sadik Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Litinin a Kano.

    • Wang Yi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Ministar Harkokin Wajen Birtaniya
    • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

    Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, (NAN), ya ruwaito cewa Pregabalin magani ne da ake amfani da shi wajen rage radadi da kuma maganin cutar farfadiya, amma hukumar NDLEA ta ce a cikin ‘yan shekarun nan ya zama daya daga cikin magungunan da ake yawan amfani da su ba bisa ka’ida ba a Nijeriya.

    Da yake mayar da martani kan wannan kamen, kwamandan NDLEA a Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, ya ce an samu nasarar kwace miyagun kwayoyin ne bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa an shirya rarraba su ne a lokacin bukukuwan Eid al-Fitr da ke tafe.

    Ya ce, “Wannan samame ya dakile wani babban shiri na rarraba miyagun kwayoyi zuwa kasuwannin haramtattun kwayoyi.”

    NDLEA ta kuma bayyana cewa babban wanda ake zargi da hannu a safarar kwayoyin ya tsere, kuma yanzu haka an saka sunansa cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo.

    “Wannan kamen ya yi wa hanyar sadarwar wannan kungiyar fataucin miyagun kwayoyi babbar illa, kuma ya kare al’ummar Kano daga illolin wadannan kwayoyi,” in ji Yahaya-Lawal.

    Ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da bin umarnin shugaban NDLEA kuma babban jami’in gudanarwa na hukumar, Mohamed Buba Marwa, domin tabbatar da an samu al’umma marar miyagun kwayoyi, tare da ci gaba da yaki da sha da fataucin kwayoyi.

    Hakazalika, ya yaba wa jama’a bisa ci gaba da ba hukumar hadin kai, tare da rokonsu su rika ba da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen dakile safarar miyagun kwayoyi.

    Yahaya-Lawal ya kuma gargadi duk masu hannu a harkar safarar miyagun kwayoyi da su daina, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta gajiya ba wajen kamo masu laifi tare da gurfanar da su a gaban doka. (NAN)

    [ad_2]

    Source link

  • Mutane 3 Mafi Tasiri A Rayuwar Ƙwallon Ƙafa Ta – Osimhen

    [ad_1]

    Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Galatasaray, Victor Osimhen, ya bayyana wasu manyan ‘yan wasa uku da suka taka muhimmiyar rawa wajen da shi iya ƙwallon ƙafa.

    Ɗan wasan mai shekaru 27 ya ambaci tsohon ɗan wasan Ivory Coast, Didier Drogba, da tsohon ɗan wasan Nijeriya, Odion Ighalo, da kuma tsohon kyaftin na Super Eagles, John Obi Mikel, a matsayin waɗanda suka zama abin koyi a gare shi.

    • Madrid Da PSG Na Shirin Sayen Osimhen
    • Babu Wani Sabani Tsakanin Osimhen Da Lookman – Ndidi

    Osimhen ya bayyana hakan ne yayin wata hira kai tsaye a Twitch tare da ɗan barkwanci Carter Efe a safiyar ranar Asabar.

    A cewarsa, ya jingina nasarorinsa gaba ɗaya ga Allah, tare da cewa akwai wasu mutane da suka taimaka masa wajen daidaita rayuwarsa da ƙwarewarsa.

    “Dangane da ƙwallon ƙafa, kowa ya san ina samun ƙwarin gwuiwa daga Didier Drogba, haka kuma daga irin su Odion Ighalo,” in ji shi.

    Ya kuma tuna haduwarsa ta farko da John Obi Mikel lokacin da aka kira shi zuwa tawagar Super Eagles karo na farko.

    “Na gan shi bayan mun gama cin abinci, sai na ce masa ‘Senior man, zan zo ɗakinka.’ Sai ya ce in biyo shi nan take,” in ji Osimhen. “Ya gayyace ni zuwa ɗakinsa, sannan ya bani kuɗi. Ba zan iya faɗin adadin ba, amma ya bani kuɗi a fam.”

    [ad_2]

    Source link

  • Tankar Mai Ta Yi Mummunan Hatsari A Kogi, Gwamnati Ta Ɗauki Mataki

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhini kan mummunar hatsarin motar da ya afku a Unguwar Okunchi a Ƙaramar Hukumar Adavi. Ta kuma jaddada cewa za ta tallafa wa iyalan da abin ya shafa.

    Wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmed Tijani Oricha ta ziyarci yankin. Tawagar ta wakilci Gwamna Ahmed Usman Ododo domin jajanta wa al’umma da duba halin da ake ciki.

    • Jihar Kogi Ta Ƙaddamar Da Masu Ba Da Taimakon Fasaha
    • EFCC Ta Gabatar Da Ƙarin Hujjoji A Shari’ar Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello

    Hatsarin ya faru ne tsakanin tankar diesel da motar BUA Cement, inda gobara mai tsanani ta tashi. Wutar ta ƙone mutanen da ke cikin tankar gaba ɗaya ba tare da a gane su ba.

    Haka kuma gobarar ta lalata wata gida da masallaci, duk da cewa babu asarar rai a waɗannan wuraren. A wani lamari kuma, wata mota mai ɗauke da fasinja biyu ta gamu da hatsari sakamakon zubewar diesel.

    Mijin ya rasu nan take bayan ya rasa iko da babur ɗinsa, yayin da matar sa ke jinya a asibiti. Daga baya kuma direban motar BUA ya rasu bayan an kai shi asibiti, yayin da mataimakinsa ya tsira da rauni.

    Al’umma da shugabannin yankin sun yaba da saurin martanin gwamnati. Sun jaddada cewa an yi amfani da kayan aiki wajen share wurin da kuma rage yawan ɓarnar.

    Oricha ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ƙara inganta hanyoyi da tsauraran matakan tsaro. Ya kuma tabbatar da jajen gwamnati ga iyalan waɗanda suka rasu.

    [ad_2]

    Source link

  • ’Yansanda Sun Ceto Wani Malamin Addini Da Matasa Suka Tsare A Jihar Gombe

    [ad_1]

    Jami’an  ‘yansanda a Jihar Gombe sun ceto wani malamin addini da wasu matasa suka kulle a cikin gida a kauyen Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada.

    Rundunar ’yansandan jihar ta ce malamin, mai suna Abubakar Mahmoud Puma, mai shekaru 58 daga Karamar Hukumar Akko, an ceto shi cikin koshin lafiya bayan wasu matasa da ake zargin mambobin wata kungiya ne suka kulle shi a cikin wani gida.

    • Wang Yi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Ministar Harkokin Wajen Birtaniya
    • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

    Kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

    A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar 15 ga Maris, 2026, bayan rundunar ta samu rahoton tashin hankali a cikin al’ummar Birin Fulani.

    “Ranar 15/03/2026 da misalin karfe 0300, rundunar ta samu rahoton tashin hankali da barazanar karya zaman lafiya a Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada,” in ji Abdullahi.

    Ya bayyana cewa jami’in ’yansandan yankin (DPO) ya gaggauta tura tawagar jami’ai zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya.

    “Da isarsu wurin, an gano cewa wani Abubakar Mahmoud Puma, mai shekaru 58 daga Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, wasu fusatattun matasa sun kulle shi a cikin gida, bisa zargin cewa ya yi kalaman cin zarafi da batanci ga shugabanninsu,” in ji sanarwar.

    Abdullahi ya kara da cewa an tura malamin zuwa yankin ne domin gudanar da Tafsir na watan Ramadan na shekarar 2026, wanda hedikwatar kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatus Sunnah ta kasa da ke Jos ta tura shi.

    Ya ce jami’in ’yansandan yankin ya tattauna da matasan da suka fusata, lamarin da ya kai ga ceto malamin lafiya.

    “Jami’in ’yansandan yankin ya tattauna da matasan cikin hikima. Bayan wannan shiga tsakani, matasan suka ba da hadin kai, aka ceto malamin lafiya ba tare da ya ji rauni ba. Ba a rasa rai ba kuma an dawo da zaman lafiya a yankin,” in ji shi.

    A halin yanzu, kwamishinan ’yansandan jihar, Umar Ahmed Chuso, ya ba da umarnin a gudanar da bincike a boye domin gano musabbabin faruwar lamarin.

    “Kwamishinan ’yansandan ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin da suka jawo faruwar lamarin da kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci bisa doka,” in ji Abdullahi.

    Rundunar ’yansandan ta kuma gargadi jama’a da su guji yada labaran karya ko wadanda ba a tabbatar da su ba a shafukan sada zumunta.

    “Rundunar na jan hankalin jama’a da su guji wallafa ko yada labaran karya ko marasa tabbaci da ka iya haifar da tashin hankali ko rudar da jama’a,” in ji sanarwar.

    Har ila yau, rundunar ta tabbatar wa mazauna Birin Fulani da ma daukacin Jihar Gombe cewa an shawo kan lamarin, tare da kira ga jama’a da su rika bin hanyoyin doka wajen gabatar da koke-kokensu maimakon daukar matakan da ka iya tayar da hankalin jama’a ko karya zaman lafiya.

    [ad_2]

    Source link

  • Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur karo na biyar a watan Maris

    [ad_1]



    A karo na biyar cikin watan Maris, Matatar Dangote ta sake ƙara farashin man fetur zuwa N1,275 kan kowace lita, daga N1,175 da ake sayarwa a farkon watan.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sabon farashin ya fara aiki daga tsakar daren ranar 21 ga Maris, kamar yadda sanarwar da matatar ta aika wa ’yan kasuwa da abokan hulɗarta ta nuna.

    Rahotanni sun ce ƙarin farashin ya samo asali ne daga sauye-sauyen kasuwar mai ta duniya, musamman sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ya shafi samar da makamashi.

    Haka kuma, matatar ta ƙara farashin jigilar mai ta ruwa daga N1,512,648 zuwa N1,646,748 kan kowace tan, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 8.9 cikin ɗari.

    Bincike ya nuna cewa farashin fetur daga matatar ya tashi daga N774 a farkon watan zuwa N1,275 a yanzu, wanda ke nuna karin sama da kashi 60 cikin ɗari cikin ƙasa da makonni uku.

    Masana sun ce wannan hauhawar farashi na iya haifar da karin kuɗin sufuri da tsadar kayayyaki a faɗin ƙasar, yayin da kasuwar mai a Najeriya ke ci gaba da fuskantar sauye-sauye bayan cire tallafi.

    Duk da haka, matatar ta ce matakin ya zama dole domin daidaita farashi da halin da kasuwar duniya ke ciki, tana mai jaddada cewa abubuwan da ke haddasa hakan sun fi ƙarfin ikon ta.


    [ad_2]

    Source link

  • An Dakatar Da Chelsea Daga Sayen ‘Yanwasa

    [ad_1]

    Hukumar kula da gasar firimiya ta Ingila ta sanyawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tara mafi kololuwa da ta taba cin wata kungiya mai haskawa a gasar mafi girma a Ingila, bayan da aka nemi ta biya kudin da ya kai fam miliyan 10 da dubu 750 kodayake an janye mata haramcin sayen ‘yan wasa dangane da tuhumar da ake mata kan cinikayyar ‘yan wasa a bayan fage da kuma boye farashinsu.

    Hukumar firimiyar ta ce bincikenta ya gano cewa Chelsea ta yi wannan haramtacciyar harkalla ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2018 ta yadda cikin sirri ta yi hulda da wasu dillalan ‘yan wasa marasa rijista don shiga tsakani a cinikin ‘yanwasan da ta yi a wancan lokacin kuma babban laifi ne a dokar hukumar kwallon Ingila.

    • ADC – Jafaru Sani Ya Mika Sakon Barka Da Sallah, Ya Soki Tsare El-Rufai
    • Ministan Tsaron Nijeriya Ya Taya Al’ummar Musulmai Murnar Sallah

    Bayanai sun ce Chelsea ta ma samu sassauci ne haka zalika hukumar ta kau da kai duba da yadda kungiyar ta bayar da hadin kai wajen bincike tare da amsa laifinta, hakan ya sanya ba a kai ga rage mata maki ko kuma yin kasa da darajarta ba. Firimiya ta wallafa wasu bayanai masu shafi 28 dauke da dukkanin laifukan na Chelsea da kudin da ta kashe wajen kawo ‘yan wasan dama ‘yan wasan har da dillalan marasa rijista da aka biya kudin.

    Wasu daga cikin ‘yanwasan da Chelsea ta biya Fam miliyan 47 da rabi ta bayan fage wajen kawo su sun kunshi Eden Hazard daga Lille kana Ramires daga Benfica sai Dabid Luis shima daga Benfica sannan Andre Schurrle daga Bayer Leberkusen sai kuma Nemanj Matic wanda kungiyar ta saya daga dai  Banfica.

    Ka zalika akwai kudaden cinikin Samuel Eto’o da Williams da kuma Anzhi Makhachkaa dukkaninsu ta bayan fage da aka biya fam miliyan 19 da adubu 300. Sannan an dakatar da kungiyar ta Chelsea daga sayan matasan ‘yanwasa wadanda za su dinga bugawa a karamar kungiya na watanni tara, sakamakon samun Chelsea da karya dokar sayan matasan ‘yanwasa.

    [ad_2]

    Source link

  • Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya

    [ad_1]

    A layin kunyar da ake noma Dabinon, wanda aka sama wa sarari kamar mita shida, za a iya shuka Irin Dabino kimanin guda 112, sannan kuma,  daga mita takwas na sarari za a iya shuka Irin nomansa kianin guda 63 a kadada daya.

    Shin Za A Iya Noman Dabino A Nijeriya?

    • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Yanayin Bazara” A Brazil
    • Ministan Tsaron Nijeriya Ya Taya Al’ummar Musulmai Murnar Sallah

    Ana noman Dabino a Arewacin Nijeriya, kamar a Jihohin Kaduna, Katsina, Kano, Sakkwato, Kebbi Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Bauchi da kuma Adamawa.

    Kazalika, ana shuka shi sau biyu a duk shekara; wato a lokacin damina da kuma na rani.

    Ana Samun Karancinsa?

    Duk da cewa, ana kara samun yin nomansa da yawa, ana kuma ci gaba da samun karancinsa, musamman saboda yadda al’umma ke kara bukatarsa.

    Kamar Ban Ruwa Nawa Bishiyar Dabino Ke Bukata?

    Dabinon da aka shuka, bai cika bukatar a dinga yi masa ban ruwa bayan an shuka shi ba, musamman a lokacin kakar damina.

    A Wane Yanayi Dabino Yake Girma?

    Dabino ya fi yin girma a  yanayin zafi, haka nan kuma ya fi yin kyau a kasar noma ta Kasar Amurka da ake samun rana mai zafi.

    Kamar Zufin Rami Nawa Dabino Ke Bukata?

    Yana girma a zurfin ramin da ya kai kafa daya zuwa kafa sha daya tare kuma da santi mita daga talatin zuwa arba’in da biyar, wannan ya danganta da irin ingancin kasar noman da aka shuka shi da kuma irin yanayin, haka nan; yana kai wa daga tsawon shekara 15 zuwa 20 kafin ya kammala girma.

    A duk fannin duniya, Nijeriya ce kawai ke nomansa sau biyu a shekara, har Nahiyar Afirka ta Arewa da Gabas ta tsakiya, inda ake hasashen Dabinon ya samu asali, sannan ana yin nomansa ne a kakar noma daya.

    Dabinon da aka shuka, na fara fitar da fure ne daga watan Janairu zuwa watan Fabirairu, inda kuma yake kammala nuna daga watan Yuni zuwa watan Oktoba.

    Wanda kuma aka shuka a kakar noman damina, yana fara yin fure ne daga watan Satumba zuwa watan Oktoba, inda kuma yake kai wa munzalin a girbe shi daga watan Fabirairu zuwa watan Maris.

    Batun Shuka Shi:

    Ana amfani da Iri don shuka shi ko kuma a shuka Saiwarsa wacce ke girma zuwa Bishiya.

    Ana kuma yanko Saiwar ce daga jikin Bishiyar da ta kai daga shekara hudu zuwa biyar, inda kuma ake fara shuka shi daga watan Juli zuwa watan Satumba, haka a kadada daya ana iya samun Bishiyar Dabino kimanin 150.

    Gyaran Gona:

    Ana so a gyra gonar da za a shuka Dabino kafin ruwan damina ya fara sauka, inda ake so a yi wa gonar haro; domin ta samu danshi sosai.

    Zuba Taki:

    An fi so a zuba masa takin gargajiya da ke dauke da sindarin ‘Nitrogen’, musamman domin ya yi saurin girma.

    Ban Ruwa:

    Bishiyar Dabino na jurewa kowane irin yanayi na noma, an fi so a yi masa ban ruwa, musamman a lokacin rani.

    Cire Ciyawa:

    Ana bukatar  manomi ya tabatar ya kiyaye  wajen yin noma, musamman don gudun kada ya kamu da cututtuka ko  harbin kwari.

    Lokacin Yin Girbi:

    Ana yi masa girbi ne bayan ya kammala girman baki-daya, wato daga shekara 15 zuwa shekara 20.

    Adana Shi Bayan Girbi:

    Sabon Dabinon da aka girbe, ana adana shi a cikin na’ura mai sanyi daga sati biyu zuwa uku, ana kuma iya adana shi har zuwa tsawon wata hudu.

    Hada-haadar Kasuwancinsa:

    Dabino ne yake  tallan kansa da kansa, musamman ganin cewa, jama’a na kara bukatarsa, kana ana sarrafa shi zuwa nau’ikan wasu abin sha; kamar kunun Aya da sauran makamantansu.

    Daga Tsawon  Kafa Nawa Bishiyar Dabino Ke Girma?

    Bishiyar Dabino na kai wa tsawon kafa 20, banda ganyensa; yana kuma kai wa tsawon shekara daga 15 zuwa 20 kafin ya kammala girman.

    Har ila yau, Dabinon da ya kai tsawon shekara 100, yana iya kai wa tsawon kafa 100.

    Ana Samun Dimbin Riba A Noman Dabino

    A shekarar 2020, Kalifoniya ta samar da tan 49,300 da aka noma kadada 12,500, inda kuma a duk kadada daya aka noma tan 3.94 da kudinsa ya kai  dala 2,320 na  kowane tan daya. An kuma kiyasta yawan amfanin Dabinon da cewa; ya kai dala miliyan 114.

    [ad_2]

    Source link

  • El-Rufai Ya Yi Nasara A Kotun Ɗaukaka Ƙara Kan Gwamnatin Jihar Kaduna

    [ad_1]

    Kotun Ƙoli da ke Kaduna ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya a ƙarar Nasir El-Rufai. Ta kuma umarci a sake sauraron shari’ar daga farko.

    Hakan ya biyo bayan ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna ya shigar kan zargin almundahanar ₦400 biliyan. Shari’ar ta shafi binciken majalisar dokokin jihar Kaduna.

    • Ramadan: Kamfanin Indomie Ya Shirya Shan Ruwa A Gidajen Kwastomominsa A Kaduna
    • Bincike: el-Rufa’i Ya Kamata Majalisa Ta Gayyato Ba Tsoffin Kwamishinoni Ba – Shehu Sani

    Alƙalai uku sun yanke hukuncin cewa an tauye masa haƙƙin jin ta bakinsa yadda ya kamata. Sun jaddada cewa ba a gabatar masa da sanarwar zaman kotu yadda doka ta tanada ba.

    Mai shari’a Onyekachi Otisi ya bayyana cewa babu tabbataccen shaidar an sanar da shi. Ya ce wannan ya sa kotu ta rasa hurumin ci gaba da shari’ar.

    Kotun ta kuma yi watsi da hujjar cewa an sanar da shi ta hanyar saƙon waya. Ta ce wannan bai cika sharuɗɗan doka na sanarwa ba

    Kotun ta ce gazawar sanarwa ta hana El-Rufai damar kare kansa a gaban kotu. Ta ƙara da cewa hakan ya saba wa ƙa’idar jin ƙara cikin adalci.

    An umurci a fara shari’ar daga farko a gaban wani sabon alƙali na Babbar Kotun Tarayya. Kotun ta jaddada cewa dole a bi ƙa’idojin doka kafin ci gaba da shari’ar.

    [ad_2]

    Source link

  • Muna duba yiwuwar kammala yaƙin Iran — Trump

    [ad_1]



    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar “kammala” hare-haren soji da ake kai wa Iran, yana mai cewa sun kusa cimma manufofinsu.

    Trump ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social.

    Ya ce: “Mun kusa cim ma muradunmu, don haka muna duba yiwuwar kammala ayyukan da sojojinmu ke yi a Gabas ta Tsakiya kan Iran.”

    Ya ƙara da cewa ya kamata sauran ƙasashen duniya su ɗauki alhakin kare Mashigar Hormuz saboda muhimmancinta, yana mai cewa Amurka ba za ta ci gaba da ɗaukar nauyin hakan ita kaɗai ba.

    Tashin hankali ya ƙaru a yankin tun bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a Iran ranar 28 ga Fabrairu, wanda rahotanni suka ce sun yi sanadin mutuwar sama da mutum 1,300.

    Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da wuraren Amurka a ƙasashen Larabawa, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin.


    [ad_2]

    Source link