CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika

[ad_1]



Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya.

CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa.

Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci.

Hukumar ta bayyana cewa zuwa ranar 11 ga watan Disamba, dole a turo mata da cikakken jerin sunayen ’yan wasa, wato kwana 10 kafin a fara gasar.

Gasar za ta gudana daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga watan Janairu, wanda ƙasar Maroko za ta kasance mai masaukin baƙi, inda ƙasashe 24 za su fafata a gasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *