Gwamnatin Kano Ta Nemi A Kama Ganduje Kan Zargin Kalaman Barazana Game Da Tsaro

[ad_1]


Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci a binciki tare da kama tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, saboda maganganun da ta ce suna barazana ga tsaron jihar.

A taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a ranar Alhamis, an tattauna kan kalaman Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar ‘yan bindiga, tare da shirin ɗaukar mutane 12,000 don kafa wata sabuwar rundunar addini da ake kira Khairul Nas.

Kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce irin waɗannan kalamai na iya lalata ƙoƙarin da gwamnatin jihar da na tarayya wajen inganta tsaro.

Ya kuma ce ƙasa da sa’o’i 48 bayan kalaman, wasu ‘yan bindiga sun shiga wasu ƙauyuka a kan iyakar jihar, lamarin da ya sa ake tunanin ko lamarin na da alaƙa da waɗancan kalamai.

Gwamnatin ta jaddada cewa ba za ta yadda wani ya kafa rundunar tsaro ba.

Ta kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina yin maganganun da za su tada hankalin jama’a, tare da tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka a faɗin jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *