Buƙatun Gwamnonin Arewa maso Gabas

[ad_1]



Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewa maso Gabas zuwa fadar shugaban ƙasa domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba.

Ganawar  wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ta mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan da suka shafi yankin Arewa maso Gabas da suka haɗa da kammala muhimman ayyukan gina hanyoyin mota 17 cikin gaggawa, da kuma ci gaba da haƙo mai a rijiyoyin kan iyaka, musamman ma rijiyoyin Kolmani da tafkin Chadi.

Sauran gwamnonin da suka halarci ganawar sun haɗa da: Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da Gwamnan Ypbe, Mai Mala Buni da Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da kuma Gwamnan Taraba Agbu Keffas.

Da yake gabatar da jawabinsa a yayin taron ganawar, Gwamnan Zulum wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, ya buƙaci shugaban ƙasar da ya kammala ayyukan tituna da kuma gina muhimman hanyoyin da suka haɗa jihohi shida na shiyyar.

Hanyoyin sun haɗa da: Titin Kano zuwa Maiduguri, titin jirgin ƙasa na Fatakwal-Jos zuwa Bauchi zuwa Maiduguri, da titin Bama zuwa Mubi zuwa Yola, da titin Wukari zuwa Jalingo zuwa Yola, da titin Duguri zuwa Mansur (NNPC project, titin Bauchi zuwa Gombe zuwa Biu zuwa Damaturu da titin Damaturu zuwa Geidam da  titin Gombe zuwa Poli-Geidam, titin Gombe-Poli-Ningi da titin Bauchi zuwa Ningi da titin Bauchi-Ningi sai Damaturu-Biu.

Sauran sun haɗa da titin Alkaleri zuwa Futuk da titin Maiduguri zuwa Damboa zuwa Yola, da titin Gombe-Dukku-Darazo da titin Biu-Gombe da titin Ibi-Shamdam, titin Maiduguri zuwa Monguno-Baga da titin Maiduguri-Ngala zuwa Bama-Banki.

Gwamna Zulum ya yaba wa shugaban ƙasa, bisa jajircewar da yake yi na ƙoƙarin maido da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas, inda ya ce, “Mun gode maka da ka samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma ci gaba da yunƙurin ganin an ci gaba da yaƙi da ’yan tada ƙayar baya.

Ya kuma tabbatar wa shugaban ƙasar kan ƙudirinsu na ganin gwamnatinsa ta samar da horo na musamman ga ma’aikata don samar da fasahar ƙere-ƙere da nufin magance matsalar rashin tsaro da yankin Arewa maso Gabas ke fuskanta.

“Muna da cikakkiyar daidaituwa tare da kyakkyawan shiri na shugaban ƙasa na horar da ma’aikata da kuma samar da fasaha da nufin kawar da mummunan halin da ake ciki a cikin dazuzzuka, ta yadda za a rage ta’addanci da kuma inganta ci gaban noma tare da sabunta ajandar samar da abinci,” in ji Zulum.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *