Bukukuwan Ƙarshen Shekara: ‘Yansanda Sun Haramta Buga Bangas A Kano
[ad_1]
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta sanar da haramta buga bangas a wani ɓangare na matakan tsaro da aka ɗauka don samar da kwanciyar hankali a yayin bikin Sabuwar Shekara ta 2026.
Umarnin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda (PPRO), CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, bayan wani taron tsaro da Kwamishinan ‘Yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori ya jagoranta.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘Yansandan ya kira taron tsaro na jagororin rundunar a jihar a ranar 29 ga Disamba, 2025, domin tsara matakan tsaro na lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
“An haramta buga Bangas da makamantanta gaba ɗaya a yayin bukukuwan ƙarshen shekara,” in ji CSP Kiyawa
[ad_2]
Source link