Binciken CGTN: Galibin Amurkawa Na Ganin Darajar Dangantaka Mai Karko Da Sin
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Lahadin cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su himmatu wajen mutunta juna, da kiyaye zaman lafiya, da kuma kokarin tabbatar da hadin gwiwa ta samun nasara ga ko wane bangare a tsakanin kasashen biyu.
Wang ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a gefen taro na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14. Wani binciken jin ra’ayoyi na baya-bayan nan da CGTN ta yi a tsakanin Amurkawa 2,001, ya nuna galibi sun amince da cewa, samun zaman lafiya mai dorewa da kyakkyawan kuzari a huldar da ke tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci, tare da bayyana kwakkwaran fatan jama’a na ganin ana samun karin hadin gwiwa na cin moriyar juna, da fadada mu’amala tsakanin kasashen biyu.
Binciken ya nuna kwarin gwiwa da amincewar bangarori mabambanta game da darajar dangantakar Sin da Amurka kamar haka: kashi 83.1 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin suna ganin ci gaba da kyautata alaka da kasar Sin na da matukar muhimmanci. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)