Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi.
A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da radadin da mutane ke ciki sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa.
Sai dai ya jaddada cewa da Najeriya ba ta dauki matakan da ta dauka ba, da tuni ta shiga halin karyewar tattalin arziki.
Tinubu ya tuna da jaruman da suka kafa kasar, yana mai cewa sun yi imani da cewa Najeriya ce jagorantar bakaken fata a duniya, kasancewar ita ce kasa mafi yawan jama’a bakaken fata.
Ya ce, “Ko da ba mu cimma duk burin da kakanninmu suka yi ba, amma ba mu kauce daga kan layinsu ba. A cikin shekaru 65 da suka gabata, Najeriya ta samu ci gaba mai yawa a fannin bunkasar tattalin arziki, hadin kan al’umma da ci gaban kasa.
“Yayin da sauki ya fi ga masu suka su dinga fadin abin da ya kamata, dole ne mu gane mu kuma yi murna da ci gaban da muka samu. A yau, ’yan Najeriya na da damar samun ilimi da kiwon lafiya fiye da a shekarar 1960,” ,” in ji shi.
Tinubu ya ce lokacin da ya hau mulki, ya gaji tattalin arzikin da ya kusa durkushewa sakamakon kuskuren manufofin kudi da rashin daidaito na tsawon shekaru.
Ya ce: “Mun fuskanci zabin da ya kasance mai sauki: ci gaba da tafiya da yadda ake yi ko kuma mu dauki hanyar gyara mai tsanani. Mun zabi hanyar gyara. Mun zabi gobe fiye da jin dadin yau.”
Shugaban ya ce kasa da shekaru uku bayan daukar wadannan matakai masu wahala, an fara ganin amfaninsu.
Ya ce gwamnatinsa ta kawo karshen tallafin man fetur da kumatsarin musayar kudade da mutane ’yan kalilan ke cin moriyarsa, yawancin al’umma ba sa amfana.
“Mun karkata tattalin arzikin zuwa hanyar da kowa zai amfana, inda kudade ke tafiya zuwa fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma da muhimman ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, intanet da ayyukan tallafi.
“Sakamakon wadannan matakai, yanzu gwamnati ta samu karin kudade a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi don kula da al’umma da warware matsalolin ci gaba.”
Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin gina sabbin hanyoyi, gyara tsofaffi, da kuma gina makarantu da asibitoci.
Ya ce: “Ba mu da isasshiyar wutar lantarki don masana’antu da gidaje, ko kudaden gyaran hanyoyin da suka lalace, ko gina tashoshin jiragen ruwa, layin dogo da filayen jiragen sama masu inganci, saboda rashin zuba jari da ya kamata tun shekaru da suka wuce.”
Sai dai ya ce gwamnatinsa na gyara abubuwa:
“Ina farin cikin sanar da ku cewa mun wuce tsanani. Wahalhalun jiya sun fara sauyawa zuwa sauki. Ina murna da juriya da goyon baya da fahimtar da kuka nuna. Zan ci gaba da aiki domin ku, kuma ina sane da amincewar da kuka ba ni.
“Tattalin arzikinmu na farfadowa da sauri. GDP na zango na biyu na 2025 ya karu da kaso 4.23 cikin 100, mafi sauri cikin shekaru hudu, ya zarce hasashen IMF na kaso 3.4 cikin 100. Hauhawar farashi ta sauka zuwa kaso 20.12 cikin 100 a watan Agusta 2025, mafi kankanta cikin shekaru uku,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin bunkasa noma da tabbatar da wadatar abinci don rage farashin kayan masarufi.
Tinubu ya lissafa wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru biyu da ya ce sun hada da karuwar kudaden shiga daga bangaren da ba na mai ba, inda aka samu sama da Naira tiriliyan 20 kafin karshen Agusta 2025, samun damar zuba jari a fannin tattalin arziki da shirye-shiryen tallafi bayan cire tallafin man fetur, karuwar kudaden ajiyar kasashen waje zuwa biliyan $42.03, mafi girma tun 2019
Ya kuma yi ikirarin cewa Najeriya na sayar da kaya fiye da yadda take saya daga kasashen waje, wanda ke karfafa kudin kasar da samar da ayyukan yi.
Tinubu ya kuma ce kayayyakin da aka kera a Najeriya da aka fitar sun karu da kaso 173 cikin 100, yayin da fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya kai kaso 48 cikin 100, yayin da na mai ke da kaso 52 cikin 100.
Ya ce hakan na nuna cewa ana karkata tattalin arzikin kasar daga dogaro da mai zuwa bangarori daban-daban.
Dangane da tsaro, Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin inganta tsaro don bunkasa tattalin arziki.
Ya ce: “Sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki tukuru don kare kasar. Sun samu nasarori a yaki da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran laifuka. Muna ganin nasarorinsu a cikin aikace.
“An samu dawowar zaman lafiya a daruruwan al’ummomin da aka ’yanta a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, inda dubban mutane suka koma gidajensu lafiya,” in ji Shugaba Tinubu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link