Barcelona ta karɓe ragamar teburin La Liga daga hannun Madrid
[ad_1]
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa Barcelona ta koma jan ragamar teburin La Liga, bayan ta doke Levante da ci 3-0 a wasan mako na 25 da aka buga ranar Lahadi a filin Camp Nou.
Barcelona ta ci ƙwallayenta ta hannun Marc Bernal da Frenkie de Jong tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, yayin da Fermín López ya ƙara ta uku a ƙarshen wasan.
Da wannan sakamakon, Barcelona ta samu maki 60, ta koma kan gaba da tazarar maki ɗaya a kan babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid, wadda ke matsayi na biyu.
Nasarar da Barcelona ta samu ta zo ne bayan ta fuskanci jerin sakamako marasa daɗi a makonnin baya, lamarin da ke nuna ƙoƙarin ƙungiyar na dawo da daidaito da ƙwazo a fafatawar neman kambun La Liga a wannan kakar.
Ita kuwa abokiyar hamayyarta, Real Madrid, ta yi tuntuɓe a wasanta na mako na 25, inda ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Osasuna ranar Asabar, lamarin da ya bai wa Barcelona damar karɓar ragamar jagorancin teburin gasar ta Sifaniya.
A tsakiyar mako kuma, Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Benfica a wasan neman gurbin zuwa zagaye na gaba a gasar Champions League.
A wasan farko da aka buga a ƙasar Portugal, Real Madrid ta yi nasara, sai dai wasan ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ɗan wasan Real, Vinícius Junior, ya yi zargin an yi masa kalaman wariyar launin fata, inda hukumar UEFA ke ci gaba da bincike kan lamarin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link