Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
[ad_1]
Tsohon jakadan Jamhuriyar Nijar a kasar Canada Abdou Boubacar, ya ce baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice, ya zamo muhimmin dandali na bunkasa kasuwancin duniya, wanda ke wanzar da salon hadin gwiwa na cimma moriyar juna.
Kalaman na Abdou Boubacar na zuwa ne yayin da ake daf da bude baje kolin na CIIE karo na takwas, inda ya ce baje kolin na samar da managartan damammaki ga masu sarrafa hajoji na kasa da kasa, da karfafa matsayin Sin na kasancewa babbar budaddiyar kasuwar duniya.
Tsohon jakadan ya kara da cewa, “Nahiyar Afirka na da fifiko a fannin samar da wasu albarkatun gona irinsu koko, da kofi, da barkono, da zuma, da man ja, da kayayyakin fasahohin hannu. Wannan kyakkyawar dama ce gare mu, ta nuna karfin nahiyar Afirka”. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link