Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay

[ad_1]



Iyalan marigayi Herbert Macaulay sun soki matakin gwamnatin tarayya na haɗa sunan fitaccen ɗan gwagwarmayar cikin riƙaƙƙun masu laifi a jerin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa bayan ransu.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Alhamis, iyalan tare da goyon bayan dattijo kuma Atona Oodua na Yarabawa, Chief Olabode George, sun bayyana cewa kodayake sun yaba da yadda shugaban ƙasa ya girmama rawar da Macaulay ya taka a tarihin Najeriya, ba daidai ba ne kuma abin ƙasƙanci ne a haɗa shi da wasu da ake tuhuma da manyan laifuka.

“Idan za a girmama Baba, to a girmama shi ne shi kaɗai,” in ji George a madadin iyalan Macaulay.

Ya ƙara da cewa, “Herbert Macaulay ba barawo ba ne; ya kasance ɗan ƙasa na gari, mai hangen nesa, kuma jikan Bishop Anglican na farko a Afirka. Ya cancanci a ware shi don girmamawa ta ƙasa, ba a haɗa shi da masu laifi ba.”

Daga cikin iyalan da suka halarci taron akwai Erelu Adeola Macaulay, Mr. Lanre Oshodi, Ms. Mayokun Thomas, Miss Kofoworola Macaulay, Miss Adeyinka Macaulay, Mr. Ayo Ogunlana, da Miss Turi Akerele, da sauransu.

A cikin jawabin sa mai taken “Herbert Macaulay: Uban Gwagwarmayar Siyasar Najeriya”, George ya ce gudummawar da Macaulay ya bayar a matsayin ɗan gwagwarmaya, injiniya, da jagoran siyasa har yanzu tana da tasiri.

Ya ce Macaulay ne ya kafa tubalin wayewar siyasar zamani a Najeriya.

“An haifi Herbert Macaulay a shekarar 1864 cikin zuri’ar ilimi, addini da hidima. Da ya so, zai iya yin shiru a tsarin mulkin mallaka, amma sai ya zaɓi ya tsaya tsayin daka wajen adawa da zalunci da faɗa da ƙarya,” in ji George.

Ya bayyana yadda Macaulay ya yi amfani da jaridar Lagos Daily News wajen yaɗa manufofinsa, yadda ya kare Oba Eshugbayi Eleko daga mulkin mallaka, da kuma yadda ya kafa jam’iyyar NNDP a shekarar 1923, jam’iyyar siyasa ta farko a Najeriya.

“Siyasar Macaulay ba ta dogara da gata ba, sai dai manufa. Ya fitar da siyasa daga ɗakunan taron turawa zuwa tituna da kasuwannin tsibirin Legas,” in ji George.

Iyalan da magoya bayansu sun bukaci gwamnati da ta girmama Macaulay ta hanyoyi na musamman, kamar kafa wuraren tunawa da shi, bayar da guraben karatu, da shirye-shiryen horar da matasa bisa ƙa’idodin da ya tsaya kai da fata a kansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *