APC ta lashe zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Kano
[ad_1]
Jam’iyyar APC ta yi nasara a zaɓukan cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da aka gudanar a ƙananan hukumomin Ungogo da Kano Municipal a ranar Asabar.
A Ƙaramar Hukumar Birni wato Kano Municipal, ɗan takarar APC, Aliyu Nabil Daneji, ya samu ƙuri’u 7,484, inda aka ayyana shi a matsayin wanda zai wakilci mazaɓar a Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Baturen Zaɓen, Farfesa Ibrahim Tajo Siraj ne ya sanar da sakamakon da ayyana Daneji a matsayin wanda ya yi nasara.
Haka kuma, Baturen Zaɓen na mazaɓar Ungogo, Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, ya bayyana cewa ɗan takarar APC, Aminu Sa’ad Sa’ad, ya samu ƙuri’u 8,975, lamarin da ya ba shi nasarar lashe kujerar.
Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa manyan jam’iyyun adawa kamar NNPP, PDP da ADC ba su shiga zaɓen ba, domin ba su gabatar da ’yan takara.
Wannan lamari ana zargin cewa ya taka rawa wajen samun ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a yawancin rumfunan zaɓe.
Kwamishinan Zaɓe na Hukumar INEC a Kano, Ambasada Abdu Zango, ya danganta ƙarancin fitowar masu zaɓen da lokacin da aka gudanar da zaɓen, da kuma ƙarancin jam’iyyun da suka shiga takara.
Sai dai ya yaba da zaɓen wanda ya bayyana a matsayin mai zaman lafiya, la’akari da cewa ba a samu rahoton tashin hankali ko barazanar tsaro ba.
Zango ya ƙara da cewa rashin shigar wasu jam’iyyun adawa ba laifin INEC ba ne, yana mai jaddada cewa duk jam’iyyar da ta bi ƙa’idojin doka da na hukumar zaɓe tana da ’yancin shiga takara.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link