Ana Samun Nasara A Yaƙi Da Cutar Fuka Da Kuturta A Jihar Zamfara
[ad_1]
Shirin Kula da Cutar Tarin Fuka, Kuturta da Buruli Ulcer na Jihar Zamfara ya samu gagarumar nasara wajen gano cututtuka, kula da marasa lafiya da kuma rigakafi.
An bayyana wannan nasara ce a yayin taron bitar aiki na kowane kwata da aka yi da ƙungiyoyin ƙananan hukumomi a Fulbe Villa Hotel, Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
- Zamfara: PDP Ta Yaba Wa Kotun Abuja Kan Nasarar Da Ta Samu
- Gwamnatin Zamfara Ta Ɓullo Da Shirin Amfana Da Ma’adanai Ga Al’umma Jihar
Taron ya haɗa jami’an shirin, masu kula da tarin fuka a ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin nazartar ci gaba da kuma inganta ayyukan ba da lafiya.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar Zamfara, Nafisa Muhammad Maradun, ta ce shirin ya ƙara ƙaimi wajen neman masu cutar a dukkan matakan kula da lafiya, lamarin da ya kai ga samun kashi 99 cikin 100 na nasarar jinya da kuma rajistar kashi 100 cikin 100 ga duk marasa lafiyar da aka gano.
“Bayanan da muka tattara sun nuna ƙarin kashi 27 cikin 100 na gano sabbin masu cutar tarin fuka a shekarar 2025 idan aka kwatanta da 2024. Haka kuma, gano tarin fuka a cikin yara ya ƙaru da kashi 47 cikin 100 a wannan lokaci,” in ji Kwamishiniyar.
Shirin ya kuma raba motocin aiki da babura domin tallafa wa sa ido, bibiyar ayyuka da kuma wayar da kai a cikin al’umma, tare da gudunmawar masu tallafa wa shirin.
Dr. Nafisa Maradun ta ce ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗa ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da aiwatar da ayyukan shirin yadda ya kamata a faɗin jihar.
“Daga zangon uku na shekarar 2024 zuwa zangon biyu na 2025, an yi wa marasa lafiya 8,891 rajista domin jinya, inda 4,769 maza ne, yayin da 4,122 mata ne. Daga cikinsu, 8,802 sun warke kuma sun kammala jinyarsu, wanda ya nuna kashi 99 cikin 100 na nasarar jinya.
Adadin mutuwa ya tsaya a kashi 0.7 cikin 100, yayin da waɗanda suka daina jinya suka kai kashi 0.3 cikin 100,” in ji ta.
Kwamishinar ta ƙara da cewa a cikin wannan lokaci, an tantance mutum 404,098 domin cutar tarin fuka, inda 125,935 ake tunanin da yiwuwar za su ɗauki cutar, sannan 10,006 aka tabbatar da suna da cutar.
[ad_2]
Source link