An soke gasar Formula One a Bahrain da Saudiyya saboda yaƙin Iran
[ad_1]
Hukumar kula da gasar tseren mota ta duniya Fédération Internationale de l’Automobile (FIA) ta sanar da soke gasar Formula One da aka shirya yi a Bahrain da kuma Saudiyya sakamakon yaƙin da ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
FIA ta ce bayan nazari mai zurfi, an yanke shawarar cewa gasar Bahrain Grand Prix da aka shirya daga ranar 10 zuwa 12 ga Afrilu da kuma Saudi Arabian Grand Prix da aka shirya mako guda bayan haka ba za su gudana ba.
Hukumar ta ƙara da cewa an cimma matakin ne bayan tuntuɓar kamfanin Formula One Group, masu shirya gasar a ƙasashen da abin ya shafa da kuma ƙungiyoyin membobin ta a yankin.
Ta kuma bayyana cewa ba za a sanya wata sabuwar gasar a watan Afrilu a madadin waɗannan ba.
Yankin Tekun Fasha dai na fuskantar hare-haren jiragen marasa matuƙa da makamai masu linzami daga Iran, tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara yaƙi da Iran a ƙarshen watan Fabrairu.
Shugaban FIA, Mohammed Ben Sulayem, ya ce tsaron mahalarta gasar da ma’aikata shi ne abin da suka fi bai wa muhimmanci, don haka aka yanke shawarar soke gasannin.
Ya ƙara da cewa Bahrain da Saudiyya na da muhimmiyar rawar da za su taka a jadawalin gasar Formula One, kuma suna fatan komawa yin gasanni a ƙasashen biyu da zarar yanayin tsaro ya daidaita.
A halin yanzu, gasar Japanese Grand Prix za ta gudana daga 27 zuwa 29 ga Maris, yayin da gasar ta gaba za ta kasance Miami Grand Prix daga ranar 1 zuwa 3 ga Mayu.
Haka kuma an soke wasannin Formula 2, Formula 3 da F1 Academy da aka shirya gudanarwa a Bahrain da Saudiyya.
Bugu da ƙari, gasar World Endurance Championship (WEC) da aka shirya yi a Qatar a ƙarshen watan Maris ita ma an ɗage ta zuwa watan Oktoba sakamakon rikicin yankin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link